A ranar 11 ga wata, an yi girgizar kasa mai karfin digiri 8.9 bisa ma'aunin
Richter a kasar Japan, lamarin da ya haifar da mummunar igiyar ruwa ta Tsunami, wacce ta haddasa mutuwar mutane a kalla 29, tare da jikkatar wasu daruruwa, kuma an dakatar da tashoshin nukiliya da daina sifirin jiragen kasa, kana an rufe babban filin jiragen sama na Narita.
Banda wannan kuma, a wannan rana, firaministan kasar Japan Naoto Kan ya yi jawabi ta gidan talabijin, inda ya yi kira ga jama'ar kasar da su yi hakuri, kuma ya bayyana cewa, gwamnatinsa za ta yi iyakacin kokari don rage barnar da girgizar kasa ta kawo. Haka kuma, ya bayyana cewa, yanzu, tashoshin nukiliya na kasar suna cikin yanayi mai kyau. (Bako)