in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin tana son jama'a su kashe kudi domin bunkasa tattalin arziki
2011-03-11 18:47:06 cri
Ibrahim: A bana, gwamnatin kasar Sin za ta kara mai da hankali kan yadda za ta bunkasa tattalin arziki ta hanyar biya bukatu cikin gida. Bayan an shiga sabuwar shekara ta 2011, sakamakon kasancewar Ranar farko ta Sabuwar Shekara da bikin bazara, wato ranar murnar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar, kasuwannin kasar Sin sun samu ci gaba sosai, har ma a wasu birane, an soma kashe kudi a wasu sabbin fannoni. Malam Sanusi, ka ga, wannan kyakkyawan mafari ne ga kokarin bunkasa tattalin arzikin kasar a bana, wannan ya kuma alamta cewa, yadda ake kashe kudi zai taka muhimmiyar rawa a cikin shekaru 5 masu zuwa a nan kasar Sin.

Sanusi: e, haka ne, malam Ibrahim. Ka sani, a nan kasar Sin, Ranar farko ta Sabuwar Shekara da Ranar bikin Bazara ta Gargajiya ranuka biyu ne da jama'ar kasar Sin suka fi son kashe kudi domin sayen kayayyakin murnar sabuwar shekara. Bisa kididdigar da ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta samu, an bayyana cewa, a cikin kwanaki 7 daga ran 2 zuwa ran 8 ga wata, wato a lokacin da jama'ar kasar Sin suke murnar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, yawan kudin da suka kashe a kasuwa da dakunan cin abinci ya kai kudin Sin yuan biliyan 404.5, wato ya karu da kashi 19 cikin dari bisa na makamancin lokaci na bara. Sannan kayayyakin da suka saya domin murnar sabuwar shekara sun sauya, yanzu mutane da yawa sun fi son sayen kayayyakin ado da aka yi da zinariya da azurfa da lu'ulu'u, wasu kuma sun sayi na'urorin lantarki masu inganci kuma masu tsada, har ma wasu daga cikinsu sun je yawon bude ido a kasashen waje.

Ibrahim: a wasu biranen da suke bakin teku, inda ake kokarin bunkasa sana'ar yawon bude ido, jiragen ruwan nishadi suke samun karbuwa a tsakanin masu yawon bude ido. Sabo da haka, yanzu ana kokarin kafa wata kasuwar cinikin kananan jiragen ruwan nishadi a birnin Xiamen dake gabas da bakin tekun kasar Sin. A shekarar da ta gabata, an sayar da irin wadannan jiragen ruwan nishadi 84 da yawan kudinsu ya kai fiye da kudin Sin yuan miliyan dari 4. Mr. Cai Zhibing, babban direktan kamfanin sayar da jiragen ruwan nishadi na Xiamen ya ce, lokacin bazara, wato daga watan Faburairu zuwa watan Mayu na kowace shekara, kyakkyawan lokaci ne na sayar da jiragen ruwan nishadi. Tun daga watan Nuwamba na bara, kamfaninsa ya riga ya fara samun kwangilolin sayen jiragen ruwan nishadi da yawa. Sabo da haka, Mr. Cai ya soma gina kananan tasoshin jiragen ruwa 400 a bana.

"Za mu kammala aikin gina tasoshin jiragen ruwa da sauran ayyukan dake da nasaba da jiragen ruwan nishadi, kamar tashar sayar da man fetur. Sannan, za mu yi kokarin tuntubar hukumomin Jinmen da Penghu na lardin Taiwan a kokarin kafa wata hanyar ruwa a tsakaninsu da birnin Xiamen. Sakamakon haka, masu yawon bude ido za su iya tuka jiargen ruwan nishadi a tsakanin birnin Xiamen da wadannan wurare biyu ta wannan hanya."

Sanusi: a cikin 'yan shekarun nan, kasuwar cinikin jiragen ruwan nishadi ta samu ci gaba cikin sauri a wasu biranen dake bakin teku. Sabo da haka, yawan manyan tasoshin jiragen ruwa da wasu birane suke son ginawa domin kananan jiragen ruwan nishadi ya kai kimanin 150. Idan za a iya yin amfani da wadannan tasoshin ruwa kamar yadda ake fata, ko shakka babu yawan jiragen ruwan nishadi da ake sayarwa zai karu.

Ibrahim: Ai malam Sanusi, ba ma kawai ana son wasa da jiragen ruwan nishadi ba, har ma an fi son wasa da wasu sabbin ayyukan yawon bude ido. Mr. Liang Zhiyi, wanda ke kula da yawon bude ido a kasar Sin a kamfanin yawon bude ido na Guangzhou ya ce, "Idan ba a son shiga wata kungiyar masu yawon bude ido, sannan kuma ana son yawon bude idon da kansa cikin 'yanci, ba damuwa, muna kuma ba da hidimar taimakawa wajen sayen tikitocin jirgin sama da yin odar otel da tarbarsa a filin jiragen sama, bugu da kari, za mu tsara masa hanyoyin yawon bude ido kamar yadda ya kamata. Sannan, muna iya samar masa tikitin jin dadin idon ruwa na zafi dake bulbulowa kyauta."

Sanusi: ba ma kawai kamfanonin yawon bude ido suna kokarin samar wa masu yawon bude ido kyawawan hidimomi ba, wasu kantuna ma suna kokarin biyan bukatun da mazauna birane da masu yawon bude ido suke da shi. Madam Pan Yunyu wadda ke kula da kantin Youyi na Guangzhou ta bayyana da harshen Guangzhou cewa, "A cikin kwanaki 7 da suka gabata, wato a lokacin da ake murnar ranar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, yawan mutanen da suka ziyarci kantinmu ya ninka sau 10 bisa na ranukan Asabar da Lahadi na yau da kullum. An yi hasashen cewa, yawan kudin sayayya zai karu da kashi 20 zuwa kashi 30 cikin dari bisa na makamancin lokaci na bara."

Ibrahim: Bisa kididdigar da hukumar yawon bude ido da sauran hukumomin kasar Sin suka yi, an ce, a cikin wadannan kwanaki 7 na murnar sabuwar shekara, yawan mutanen da suka shakata a duk fadin kasar Sin ya kai miliyan 153, kuma yawan kudin da suka kashe ya kai fiye da kudin Sin biliyan 82, wato ya karu fiye da kashi 20 cikin dari bisa na makamancin lokaci na bara. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China