Game da wahalhalun da ake fuskanta, Chen Zhu ya kara da cewa, a bana, ya kamata a samarwa jama'ar kasar sauki wajen ganin likitoci.
Mataimakin darektan kwamitin kula da bunkasuwa da yin gyare-gyare na kasar Sin kuma darektan ofishin al'amuran gyare-gyaren tsarin kiwon lafiya na majalisar gudanarwa ta kasar Sun Zhigang ya bayyana cewa, a bana, za a kara inganta tsarin kiwon lafiya a kauyuka.(Abubakar)