in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta cimma burinta na kafa tsarin dokokin gurguzu na musamman a shekara ta 2010
2011-03-10 11:15:50 cri

Shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Mista Wu Bangguo ya fada a wajen taron shekara-shekara na majalisar da aka yi a ranar 10 ga wata cewa, Sin ta cimma burinta na kafa tsarin dokokin gurguzu na musamman a shekarar da ta gabata wato shekara ta 2010.

A wannan rana, Mista Wu Bangguo ya gabatar da rahoton aikin kwamitin ga majalisarsa, inda ya ce, ya zuwa karshen shekara ta 2010, kasar Sin ta yi nasarar kafa wani tsarin dokokin gurguzu na musamman, wanda ya dace da hakikanin halin da ake ciki a kasar gami da manufar yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje. Haka kuma, wannan tsarin dokokin ya bayyana manufar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin gami da jama'arta, wanda ke kunshe da dokoki a fannoni da kuma matakai daban-daban, ciki har da kundin tsarin mulkin kasar, dokokin da suka shafi rayuwar jama'a da harkokin kasuwanci da sauransu.

Mista Wu Bangguo ya kara da cewa, an kafa tsarin dokokin gurguzu na musamman na kasar Sin ne bisa la'akari da ainihin halin da kasar take ciki, haka kuma ya ce, a nan gaba, kamata yayi a nuna hazaka wajen yin nazari kan yadda za'a shigar da jama'a cikin aikin kafa dokoki, da kyautata tsarin sauraren ra'ayoyin jama'a, a kokarin samun ci gaba a fannin kafa dokoki ta hanyar kimiyya da tafarkin demokuradiyya.(Murtala)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China