in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tsarin tabbacin harkokin kiwon lafiya ya shafi mutane biliyan 1.26 a kasar Sin
2011-03-09 20:39:19 cri

Mataimakin ministan kula da harkokin kwadago da tabbacin zaman al'umma na kasar Sin, Hu Xiaoyi ya bayyana a ranar 9 ga wata cewa, tsarin ba da tabbacin harkokin kiwon lafiya ya shafi mutanen da yawansu ya kai sama da biliyan 1 da miliyan 260 a kasar, kuma yanzu ana wani kokari na tabbatar da tsarin a kan dukkanin 'yan kasar.

A gun taron manema labarai da aka kira a wannan rana, Hu Xiaoyi ya ce, cikin shekaru uku da suka gabata, kudin gudummawar da hukumomin kudi na kasar Sin suke samar wa mazauna birane da garuruwa ta fannin samun inshorar kiwon lafiya ya zarce kudin Sin yuan biliyan 46, kuma adadin zai karu zuwa biliyan 106 da miliyan 800 idan aka yi la'akari da kudin gudummawar da ake samar wa ma'aikatan kasar ta fannin inshorar kiwon lafiya. Kudin ya taimaka kara adadin mutanen da ke iya samun tabbacin harkokin kiwon lafiya, wanda kuma ya daidaita matsalar samun tabbacin harkokin kiwon lafiya da ke addabar wasu ma'aikata miliyan 8 da suka yi ritaya daga masana'antun da suka rushe. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China