A gun taron manema labaru na taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin. Feng Jun ya ce, shimfidar tsarin dokoki wani mawuyancin aiki ne mafi muhimmanci, bangarorin da abin ya shafa za su yi bincike a lokacin da ya dace tare da maida hankali ga ra'ayoyin jama'a da wasu kwararru. Ya zuwa yanzu, an gudanar da wannan aiki yadda ya kamata. Kuma ana sa ran alheri kuma ana shirin tura shi majalisar gudanarwa domin samun amincewa daga majalisar wakilan jama'ar kasar bayan majalisar gudanarwa ta zartas da shi.(Amina)