Shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin Jia Qinglin ya halarci taron, a cikin jawabin da wasu wakilan majalisar da suka hada da wakilin Zhang Daning suka bayar, an ce, a 'yan shekaru da suka wuce, ba a samu ci gaba cikin sauri ba a fannin bunkasa harkokin al'ummar kasar. Ya kamata hukumomi daban daban su kara zuba jari ga harkokin al'ummar kasar, da kyautata tsarin samar da hidima ga al'ummar da kyautata tsarin kiwon lafiya da tsarin ciyar da tsoffi da taimakawa 'yan mata masu ciki da manoma da suka rasa gonaki. Da kara kyautata ingancin abinci, don kara samar da moriya ga jama'ar kasar.(Abubakar)