in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sha'anin al'adu zai zama muhimmin sashe na kasar Sin a karshen lokacin aiwatar da shiri na 12 na shekaru 5 na raya kasa
2011-03-09 09:44:44 cri

A ran 8 ga wata, ministan harkokin al'adu na kasar Sin Cai Wu ya bayyana cewa, a lokacin da ake aiwatar da shiri na 12 na shekaru 5 na raya kasa, sha'anin al'adu zai samu babban ci gaba. A shekaru 5 masu zuwa, yawan kudin da za a samu daga sha'anin al'adu zai kai kashi 5 cikin kashi dari na yawan kudin da aka samu daga sarrafa dukiyar kasa wato GDP, sabo da haka sha'anin zai zama muhimmin sashe na tattalin arziki na kasar Sin.

A ran 8 ga wata da safe, Cai Wu ya halarci taron tawagar wakilan yankin Hongkong masu halartar taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, inda ya bayyana cewa, yanzu dai yawan kudin da aka samu daga sha'anin al'adu ya kai kashi 2.6 cikin kashi dari na yawan GDP na kasar. Ya yi kiyasta cewa, yawansa zai kai kashi 5 cikin kashi dari na yawan GDP a karshen lokacin da ake aiwatar da shiri na 12 na shekaru 5 na raya kasa.

Kana Cai Wu ya furta cewa, kasar Sin tana kokarin kara zuba jari ga sha'anin al'adu.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China