A yayin da yake halartar taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da ake yi yanzu a nan birnin Beijing, Wang ya ce, jihar ta Ningxia za ta yi kokarin gudanar da taron dandalin tattaunawar harkokin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da kasashen Larabawa yadda ya kamata, kuma za ta yi kokarin zama wani muhimmin bigire na samar da abincin halal da kayayyakin musulmi a kasar Sin kana wani babban dandali na gudanar da hadin gwiwa tsakanin kasar da kasashen musulmi.
A cewarsa, ko ta fannin tarihi da al'adu ko kuma ta fannin masana'antu, jihar Ningxia tana da fifiko wajen gudanar da hadin gwiwa da kasashen musulmi, abin da ya aza harsashi mai inganci ga inganta hadin gwiwa tsakaninta da wadannan kasashen.(Lubabatu)