Yin Weimin ya bayyana cewa, a bana larduna da birane da dama za su ci gaba da duba yiwuwar karin kudin albashi. Gwamnatin kasar Sin za ta tsara ma'aunin bisa bunkasuwar tattalin arzikinta, da karuwar farashin kaya, da kuma karuwar karfin masana'antu wajen kawo albarka.
Yin Weimin ya kara da cewa, za a kafa tsarin ba da tabbaci ga al'umma da zai shafi dukkan birane da kauyuka a lokacin da ake gudanar da shiri na 12 na neman samun bunkasuwa a shekaru biyar masu zuwa, kana kafa tsarin kudin fensho na mazauna birane zai kasance mafi muhimmanci. A sa'i daya kuma, ya kamata a kara ba da tabbaci ga manoma 'yan cin rani da kuma sauran mutanen da ba su da dawamammen aikin yi.