Ranar 7 ga wata, a wajen wani taron manema labarai da aka shirya a Beijing, ministan harkokin wajen kasar Sin Yang Jiechi ya bayyana cewa, kasar Sin kasa ce dake tasowa, kuma tana iya taka rawa gwargwadon karfinta. Hakan na nufin cewa, ko da yake kasar Sin ta kasance ta biyu a fannin tattalin arziki a duniya, amma ita ba wata kasa ce mai karfi ba, kuma tana fuskantar wahalhalu da matsaloli da dama a yayin da take kokarin neman ci gaba, don haka kamata yayi nauyin da kasar Sin ke dauka ya dace da halin da ake ciki a kasar.
Kwanan baya, kafofin watsa labaran duniya sun ruwaito wani labarin dake cewa, kasar Sin ta kasance ta biyu a fannin tattalin arziki a duniya bayan da ta wuce kasar Japan, shi ya sa ake ganin wai ya kamata kasar Sin ta kara daukar nauyin dake kanta.
1 2 3