in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jihar Xinjiang tana cikin hali mai kyau, a cewar Nur Bekri
2011-03-08 15:07:30 cri

A ran 8 ga wata, shugaban jihar Xinjiang mai cin gashin kanta ta kabilar Uygur Nur Bekri ya ce, yanzu haka ana ciki hali mai kyau a jihar Xinjiang.

Nur Bekri ya ce, tun daga watan Yuli na bara, sa'anar yawon shakatawa ta jihar Xinjiang ta samu bunkasuwa cikin sauri. Yawan mutanen sauran wuraren kasar Sin da suka je yawon shakatawa a jihar a shekarar bara ya kai miliyan 30, kana yawan mutanen kasashen waje da suka tafi jihar ya kai fiye da miliyan daya, a sakamakon haka, yawan kudin da aka samu daga wajen masu yawon shakatawa na kasashen waje ya kai dalar Amurka miliyan 300, wanda ya karu da kashi 40 cikin dari idan aka kwatanta da makamacin lokacin shekarar 2009.

Nur Bekri ya kara da cewa, idan ba a tabbatar da zaman lafiya ba, ba za a kyautata zaman rayuwar mutanen jihar Xinjiang ba. Ko ta wane hali, dole ne a mayar da aikin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a matsayin aiki mafi muhimmanci.

Duk da haka, Nur Bekri ya bayyana cewa, ana fuskantar kalubale da yawa a fannin tabbatar da zaman lafiya a jihar Xinjiang.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China