in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Daga wata sabuwar memba zuwa wadda ke kokarin ciyar da harkokin WTO gaba
2011-03-07 21:42:17 cri
A ranar 7 ga wata, ministan harkokin kasuwanci na kasar Sin Chen Deming ya bayyana cewa, bayan da Sin ta shiga cikin kungiyar cinikayya ta duniya WTO, ta bunkasa daga wata sabuwar memba har izuwa wadda ke yin kokari sosai wajen ciyar da harkokin kungiyar gaba, kuma ta zama wata muhimmiyar memba a wannan kungiya.

Yayin da Chen Deming ke halartar taron manema labaru ta gefen taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'a a wannan rana, ya ce, a cikin shekaru 10 da suka gabata, Sin ta rage matsaikacin kudin kwastan da ta buga daga kashi 15.3 cikin 100 zuwa kashi 9.8 cikin 100, kuma ta bude kofar sassan cinikin harkokin samar da hidima sama da 100, kuma ta yi gyare-gyare ga dokoki sama da 3000 da ba a taba ganin irinsu ba a cikin tarihi, haka kuma, ta fahimci ka'idojin cinikayya na duniya, kuma ta kafa tsarin yin cinikayya da kasashen waje.

Chen Deming ya ce, a cikin shekaru 10 da suka gabata, ba ma kawai Sin ta samu karfi daga shiga cikin WTO da yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje ba, haka kuma ta zama tamkar wani ginshiki wajen raya tattalin arziki na duniya. A cikin shekaru 5 masu zuwa, Sin za ta ci gaba da gyaran salon raya harkokin cinikayya da kasashen waje, don bunkasa harkokin fitar da shigar da kayayyaki tare, da yalwata harkokin shigar da kayayyaki, da sa kaimi wajen daidaita rarar cinikin da ke kasancewa tsakaninta da kasashe marasa ci gaba.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China