in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin kasar Sin za ta fi mayar da hankali kan harkokin da ke shafar zaman rayuwar jama'a
2011-03-07 21:37:07 cri

Ministan kudi na kasar Sin, Xie Xuren ya bayyana a ranar 7 ga wata cewa, a shekarar 2011, gwamnatin kasar Sin za ta fi mayar da hankali kan harkokin da ke shafar zaman rayuwar jama'a.

A gun wani taron manema labarai da aka kira a gefen taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da ake yi yanzu a birnin Beijing, Mr.Xie Xuren ya ce, kudin da gwamnatin kasar Sin ta ware kan harkokin da ke shafar zaman rayuwar jama'a zai dauki kimanin kashi biyu daga cikin uku na kudin da za ta yi amfani da su a bana, kuma daga cikinsu, yawan kudin da za ta biya kan harkokin ilmi, kiwon lafiya, gidajen zama domin masu masu karamin karfi, al'adu, ba da tabbacin zaman rayuwar al'umma da samar da guraben aiki da sauransu zai kai kimanin kudin Sin yuan biliyan 1050, wanda zai karu da kashi 18.1% bisa na shekarar bara. Ban da wannan, yawan kudin da gwamnatin kasar Sin za ta ware ta fannonin ayyukan gona da ban ruwa, zirga-zriga da kiyaye muhalli ma zai karu. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China