in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kafofin watsa labaru na kasashe daban daban sun mai da hankali kan yadda gwamnatin kasar Sin za ta yi kokarin kara tabbatar da jin dadin jama'a
2011-03-07 21:10:16 cri
A lokacin da ake gudanar da tarurrukan shekara-shekara na majalisun kasar Sin, kafofin watsa labaru na kasashe daban daban suna mai da hankali kan al'amuran dake wakana, har ma sun ba da labarin cewa 'yadda za a kara tabbatar da jin dadin jama'a' zai zama wani babban jigon da gwamnatin kasar Sin za ta mai da hankali a kai wajen ayyukan da za ta gudanar a gaba.

Kamfanin dillancin labaru na Associated Press na kasar Amurka ya ba da labarin cewa, jin dadin jama'a ya zame wa gwamnatin kasar Sin wani babban jigo daga cikin ayyukan da take kula da su, don haka gwamnatin za ta yi kokarin dakile hauhawar farashin kaya, da tabbatar da wata hanya mai dorewa wajen raya tattalin arziki.

Jaridar The Daily Telegraph ta kasar Birtaniyya ta ba da labarin cewa, gwamnatin kasar Sin ta samar da wani ma'auni don tantance hazakar jami'an kasar wajen gudanar da harkokin mulki, wanda shi ne 'tabbatar da jin dadin jama'a', hakan ya shaida cewa, 'kula da zaman rayuwar jama'a' ya maye gurbin 'kara saurin bunkasuwar tattalin arziki' wajen zama mizani mai muhimmanci ta fuskar jarraba jami'ai.

Kana jaridar Financial Times ta kasar Birtaniya ta bayyana cewa, yadda kasar Sin ta kayyde karin GDP din kasar a shekaru 5 masu zuwa kan matsayin kashi 7%, jimillar da ta ragu bisa ta baya, lamarin da ya shaida wani babban sauyin yanayi dangane da manufar kasar. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China