in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kafa dangantakar hadin gwiwa dake tsakanin Sin da Amurka ya dace da moriyar kasashen biyu
2011-03-07 15:33:16 cri

A ran 7 ga wata, ministan harkokin waje na kasar Sin Yang Jiechi ya bayyana cewa, kasashen Sin da Amurka manyan kasashe ne a duk fadin duniya, sun tsai da kudurin kulla dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa a tsakaninsu, wannan ya dace da halin da ake ciki a yanzu, kana ya biya bukatun kasashen biyu wajen zurfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu.

A gun taron manema labaru da aka yi a birnin Beijing, Yang Jiechi ya ce, shugabannin kasashen Sin da Amurka sun cimma daidaito kan yadda za a inganta hadin gwiwa dake tsakaninsu. Kamata ya yi a gudanar da ayyukan da shugabannin kasashen biyu suka tsara don inganta dangantakar abokantaka dake tsakaninsu. Ban da wannan kuma, ya bayyana cewa, akwai wasu bambancin ra'ayoyi kan wasu batutuwa a tsakanin Sin da Amurka, duk da haka, ya kamata kasashen biyu su girmama juna da warware matsalolin dake tsakaninsu yadda ya kamata.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China