in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta tsara shirin neman samun bunkasuwa mai dorewa da wadatar da jama'a a shekaru biyar masu zuwa
2011-03-07 13:29:03 cri

Wakilan jama'a kimanin dubu 3 na kasar Sin suna tattauna shiri na 12 na neman samun bunkasuwa na shekaru biyar wato daga shekarar 2011 zuwa shekarar 2015 domin kara samun bunkasuwar al'umma ba tare da gurbata muhalli ba da kuma kara wadatar da jama'a. A ran 6 ga wata, jami'an kwamitin kula da harkokin bunkasuwa da gyare-gyare na kasar Sin sun tantance wannan shiri, daga baya sun bayyana cewa, ba a kayyade saurin bunkasuwar tattalin arzikin kasar a cikin shekaru biyar masu zuwa ba, amma ana kara dora muhimmanci kan gyara hanyar bunkasa tattalin arziki da kara kyautata zaman rayuwar jama'a, ta yadda dukkan jama'ar kasar Sin za su kara cin gajiyar sakamakon da aka samu wajen neman bunkasuwar kasar.

Tattalin arzikin kasar Sin ya shafe shekaru fiye da 30 yana samun bunkasuwa cikin sauri, matsakaicin yawan karuwar GDP a shekaru biyar da suka gabata ya kai kashi 11.2 cikin dari, yawan GDP a shekarar bara ya kai kudin Sin RMB biliyan dubu 39. Amma shirin neman bunkasuwa na 12 da aka gabatar bai kayyade saurin bunkasuwar tattalin arziki ba. Darektan kwamitin kula da harkokin bunkasuwa da gyare-gyare na kasar Sin Zhang Ping ya ce, kasar Sin ta kara dora muhimmanci kan ingancin bunkasuwar tattalin arziki amma ba saurin bunkasuwarsa ba. Mr. Zhang ya ce, "Bisa shirin da muka tsara, ya kamata mu gaggauta gyara hanyar bunkasa tattalin arziki da kara ingancin ci gaban tattalin arziki. Sabo da haka, ba mu kayyade saurin neman samun bunkasuwar tattalin arziki ba."

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China