in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Daga ci gaban tattalin arziki zuwa ci gaban zaman al'umma: nazari kan wasu alkaluma cikin shiri na 12 kan bunkasa tattalin arziki da zaman al'umma a kasar Sin
2011-03-06 19:11:34 cri

"Ina fatan sararin sama zai kara shudi a birnin Beijing, kuma ina fatan iskar da muke shaka za ta kara inganci."

"Ina fatan farashin kayayyaki zai koma yadda ya kamata, kuma kudin shigar jama'a zai karu."

"Ina fatan farashin gidaje zai sauka zuwa wani farashin da ya dace."

Ra'ayoyin wasu 'yan kasar Sin ke nan da muka samu a kan titunan birnin Beijing, suna bayyana burinsu kan zaman rayuwa. Kamar yadda jama'a ke yin kira da a kyautata musu zaman rayuwa, daftarin shiri na 12 kan bunkasa tattalin arziki da zaman al'umma a kasar Sin cikin shekaru biyar masu zuwa, wanda yanzu haka ake duba shi a gun taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar, shi ma ya bayyana wani babban jigo na kyautata zaman rayuwar jama'a da jin dadinsu. "nan da shekaru biyar masu zuwa, burin da za mu yi kokarin cimma ta fuskar tattalin arziki shi ne, ya karu da kashi 7% a kowace shekara tare kuma da kara samun inganci." "matsakaicin kudin shigar mazauna birane da karkara zai karu da sama da kashi 7% a kowace shekara." "Fadin gidaje domin masu samun kudin shiga mafi kankanta zai kai kimanin kashi 20% na fadin gidaje a birane da garuruwa na kasar."

Wannan bayani ne da firaministan kasar Sin, Wen Jiabao ya yi dangane da shiri na 12 kan bunkasa tattalin arziki da zaman al'umma cikin shekaru biyar masu zuwa a yayin da yake mika rahoton aikin gwamnati a gun taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da ake yi yanzu a birnin Beijing. Masana suna ganin cewa, wadannan alkaluman da aka bayyana cikin shirin suna nuni da sauyin hanyar neman ci gaba a kasar, wato baya ga saurin karuwar GDP, nan da shekaru biyar masu zuwa, kasar za ta juya hankalinta a kan ingancin tattalin arziki da samun moriyar al'umma da ci gaban tattalin arziki da kuma kara mai da hankali a kan ci gaban al'umma.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China