A gun taron manema labaru da aka yi dangane da taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'a, Zhang Ping ya bayyana cewa, a lokacin shirin samun bunkasuwa na shekaru biyar-biyar a karo na 12, za a yi kokarin kiyaye ka'idar mayar da aikin raya zaman rayuwar al'umma a gaban kome, kuma kamata ya yi a tabbatar da ganin jama'ar kabilu daban daban na kasar sun samu moriyar irin nasarorin da aka samu wajen yin gyare-gyare da samun bunkasuwa.
Zhang Ping ya ce, an mayar da samun bunkasuwa a gaban kome yayin da aka tsara shirin samun bunkasuwa na shekaru biyar-biyar a karo na 11, kuma wannan ya zama wajibi a yi hakan. Saboda wancan lokaci, ba a warware matsalar samar da isasshen abinci ba, kuma ba a samu wadatar kayayyaki a kasar ba, ya zama dole ne a tabbatar da raya tattalin arzikin kasar. Amma yanzu, ana samun isassun kayayyaki, kamata ya yi a kara mai da hankali wajen kyautata zaman rayuwar al'umma, kuma a cikin shirin samun bunkasuwa na shekaru biyar-biyar a karo na 12, an tsaida shirye-shirye da bukatu da dama, game da raba kudin shiga da samar da guraben aikin yi da yin hidima, da aikin jinya, da ilmi da tabbatar da zaman rayuwar al'umma.(Bako)