Mista Zhang ya ce, yawancin kayayyakin da ake samarwa daga masana'antun kasar Sin, yawansu ya wuce jimillar da ake bukata a kasuwa.
Ban da haka kuma, Li Yining, dan majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin, kana shahararren masanin ilimin tattalin arziki na kasar, ya bayyana a ranar 6 ga wata a nan birnin Beijing cewa, matakan da kasar Sin ke dauka a halin yanzu don dakile hauhawar farashin kaya suna da amfani.
A wajen wani taron manema labaru da aka yi a gefen taron shekara-shekara na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin, Li Yining ya ce, akwai dalilai da yawa da suka haddasa hauhawar farashin kaya a kasar Sin, wadda ta fara kunno kai a shekarar 2010. Amma yadda kasar ta kara yawan kudin da ya kamata bankuna daban daban su ajiye a babban bankin kasar har sau da dama, ya yi amfani sosai wajen shawo kan hauhawar farashin kaya a kasar.
Mista Li ya kara da cewa, ko da yake ba a samu damar shawo kan sharuda 2 da suke haddasa hauhawar farashin kaya ba, wadanda suka hada da karuwar farashin mai a kasuwannin duniya, gami da dumamar yanayi wadda take addabar aikin gona, amma duk da haka, ta hanyar daukar wasu matakai a gida, za a iya dakile hauhawar farashin kaya, har ma a tabbatar da dorewarsa gwargwadon wani mizani. (Bello Wang)