in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin kasar Sin za ta mayar da hankali kan kyautata zaman rayuwar jama'a a yayin da take kokarin bunkasa tsarin tattalin arziki
2011-03-05 16:54:29 cri
An bude taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a ranar 5 ga wata a nan birnin Beijing, inda wakilai kusan 3000 da suka fito daga wurare daban daban suka taru a babban dakin taro na jama'ar kasar Sin, domin tattauna shirin ci gaban tattalin arzikin kasar a nan gaba.

Firaministan kasar Sin, Wen Jiabao ya karantawa wakilan jama'a wani rahoto game da ayyukan da gwamnatin kasar ta yi. Da farko ya bayyana manufar da gwamnatin kasar za ta dauka a cikin shekaru biyar masu zuwa.

'Za mu yi kokarin kara bunkasa tattalin arziki zuwa wani sabon matsayi. A cikin shekaru biyar masu zuwa, matsakaicin karuwar tattalin arziki zai karu da kashi 7 cikin kashi 100 a ko wace shekara lokacin da kasar take kokarin tabbatar da ingancinsa. Yawan kudin da aka samu daga sarrafa dukiyar kasar zai wuce RMB biliyan 55000 a shekara ta 2015. Za mu yi kokarin kyautata zaman rayuwar jama'a da zurfafa aikin yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje a dukkan fannoni,'

A cikin rahoton kuma, Wen Jiabao ya gabatar da muhimman ayyukan dake gaban gwamnatin kasar Sin a cikin shekaru biyar masu zuwa. Ya kuma bayyana cewa, gwamnatin kasar za ta mayar da hankali kan fatan da jama'ar kabilu daban daban na kasar suke da ita wajen kyautata zaman rayuwarsu, da samun bunkasuwa ta hanyar kimiyya, da kuma kara saurin canjawar hanyar bunkasuwar tattalin arziki a yayin da take kokarin zurfafa ayyukan yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, da ba da tabbaci da kuma kyautata zaman rayuwar jama'a, kana da inganta nasarar da ta samu wajen magance matsalar kudi ta duniya, da ciyar da bunkasuwar tattalin arziki gaba yadda ya kamata, da kuma shimfida zaman karko da neman sakamako mai kyau na zamantakewar al'umma, ta yadda za a aza harsashi mai kyau ga tabbatar da zaman al'umma mai wadata.

A cikin shekaru biyar da suka wuce, matsakaicin kudin da aka samu daga sarrafa dukiyar kasar Sin ya karu da kashi 11.2 cikin kashi 100 a ko wace shekara, wannan ya ba da tabbaci wajen aiwatar da shirin raya kasa na 12 na shekaru biyar-biyar da za a yi.

Amma, a sa'i daya kuma, Wen Jiabao ya bayyana cewa, babban gibin kudin shiga da jama'ar Sin ke samu, da tsarin tafiyar da masana'antun da suka sabawa doka, da sauran matsaloli su ne babban kalubalen da kasar ke fuskanta a yanzu a fannonin tattalin arziki da zaman al'umma.

Dadin dadawa, wannan rahoto ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da fuskantar hali mai sarkakiya sosai wajen neman ci gaba a shekarar 2011. Ana fatan saurin ci gaban tattalin arzikin kasar Sin zai kai kashi 8 cikin kashi dari a bana. Kuma saurin hauhawar farashin kayayyaki na yau da kullum ya kai kashi 4 cikin dari. Bugu da kari, ana fatan za a iya samar da guraban aikin yi ga mutane fiye da miliyan 90.

Wen Jiabao ya furta cewa, idan ana son cimma wadannan burin da aka ambata a baya, to ya kamata a daidaita dangantakar da ke tsakanin batun kiyaye saurin ci gaban tattalin arziki ba tare da tangarda ba, da batun daidaita tsarin tattalin arziki, kana da batun gudanar da matsalolin da ke da nasaba da hauhawar farashin kayayyaki. Kuma ya kamata a kara mai da hankali kan daidaita farashin kayayyaki domin magance tabarbarewar tattalin arziki.

A cikin rahoton aiki, Wen Jiabao ya yi bayani kan ayyukan da suka shafi batun raya zaman al'umma da kuma inganta rayuwar jama'a, inda ya bukaci gwamnatoci na matakai daban daban da su yi iyakacin kokari don warware matsalolin da ke da nasaba da muradun jama'a. Kamar yadda Wen Jiabao ya fada:

"idan an samu saurin ci gaban tattalin arziki, to ya kamata a kara dora muhimmanci kan raya zaman al'umma da kuma inganta rayuwar jama'a."

Wannan managar da Wen Jiabao ya fada ta sheda cewa, gwamnatin kasar Sin za ta kara mai da hankali kan batutuwan da ke da nasaba da zaman rayuwar jama'a. Ban da wannan kuma, daidaita dangantakar da ke tsakanin samun kudi da rarraba shi domin kara rabon kudin da aka samu ta hanyar aiki wani muhimmin aiki ne da ke gaban gwamnatin kasar Sin. Rahoton ya nuna cewa, a bana, za a dauki matakai a fannoni uku domin warware matsalar, wato za a yi kokarin kara yawan kudin shiga da mazauna birane da na yankunan karkara masu karamin karfi za su samu, kuma za a kara karfin daidaita batun rarraba kudin shiga, kana za a sa kaimi wajen kyautata dokokin da suka shafi rarraba kudin shiga.

A cikin shekaru da dama da suka gabata, hauhawar farashin dakunan kwana wata matsala ce da ke dame jama'ar kasar Sin. Game da matsalar, rahoton aiki kuma ya bayyana cewa, za a tsaya tsayin daka kan daidaita kasuwar gidajen da dakunan kwana, inda aka nuna cewa, a bana, za a kara gina gidajen kwana masu rahusa don jama'a masu karamin karfi da kuma gyara tsoffin gidaje da yawansu ya kai miliyan 10, wanda zai ninka kusan sau daya bisa na bara.

Ana iya ganin cewa, dukkan wadannan ayyuka sun shafi zaman rayuwar jama'a, wannan ya sheda cewa, yayin da kasar Sin ke jaddada muhimmancin canja hanyar raya tattalin arziki, aikin kyautata da ba da tabbaci ga zaman rayuwar jama'a kusan ya zama muhimmin aikin da ke gaban gwamnatin kasar Sin. Gwamnatin kasar Sin na daukar hakikanin matakai domin nuna cewa, kasar Sin za ta tsaya tsayin daka kan samun wadata tare, ta yadda kyawawan sakamakon da kasar ta samu ta fuskar ci gabanta za su amfana wa dukkan jama'arta.(Bilkisu Xin&Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China