in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan majalisar CPPCC suna fadi albarkacin bakinsu kan harkokin siyasa
2011-03-04 16:49:58 cri
Jiya 3 ga wata da yamma, an kaddamar da taron shekara-shekara na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin wato CPPCC, inda 'yan majalisar fiye da dubu 2 da suka fito daga sassa daban daban na kasar Sin suka taru a nan Beijing, inda za su yi shawarwari tsakaninsu da suka shafi jama'ar kasar Sin. To, sai dai batun zaman rayuwar jama'a ya sake jawo hankalin mahalata taron.

A cikin rahoton da Jia Qinglin, shugaban majalisar CPPCC ya bayar a game da ayyukan zaunannen kwamitin majalisar, dan dauko maganar jaddada da karfafa gwiwar 'yan majalisar wajen kara fahimtar zaman rayuwar jama'a, tare da ba da shawara game da wadatar da jama'a da kawo musu alheri, inda ya ce,"Ya zama dole mu tsaya tsayin daka kan mayar da dan Adam a gaban kome da sauke nauyi bisa kanmu domin bautawa jama'a, a karfafa gwiwar 'yan majalisar domin su kara kusantar jama'a, su yi ayyukan da ke amfanawa jama'a, su ba da shawarar da ke shafar wadatar da jama'a da kawo musu alheri."

Sinawa kan ce, abinci ya fi kome muhimmanci ga jama'a. Kowa na mai da hankali kan batun abinci. A bana, 'yan majalisar su ma sun mai da hankali kan ingancin abinci, saboda tilas ne a mai da hankali matuka kan lafiyar mutane. Da yawa daga cikinsu na ganin cewa, ingancin abinci na da nasaba da yadda jama'a suke jin dadin zamansu. Inda Feng Chuanjian, dan majalisar da ya fito daga lardin Hainan ya bayyana cewa,"A ganina, a sabuwar shekara wajibi ne a sa ido kan ingancin abinci, saboda baya ga samun kudin shiga, tabbatar da lafiyar jiki ya fi muhimmanci a fannin jin dadin zaman rayuwa."

Yanzu haka, Sin na bukatar kwararru a fannoni daban daban, kuma dalibai na fuskantar matsalar samun aikin yi, Lin Jialai, dan majalisar ya shawarci kwalejoji da jami'o'i su samar wa daliban da za su gama karatu lokaci da dama ta yin aiki kafin sun bar jami'o'i. Lin ya ce,"Yanzu ba a samu nasara wajen yin gyare-gyare kan tsarin tarbiya a jami'o'i ba, inda ake fi mai da hankali kan samun ilmi. Ta haka wasu kamfannoni na sha'awar yin hayar daliban da suka gama karatu daga kwalejojin koyar da sana'o'i, wadanda suka gwanance wajen kera kayayyaki da hannu, daliban da suka gama karatu daga jami'o'i kuma ko da yake suna da ilmi, amma sun rasa isasshen karfin kera kaya da hannu. Don haka na ba da shawarar samar wa ko wane dalibi wata daya ko biyu don su rika aiki kafin sun gama karatu, su yi amfani da ilminsu wajen gudanar da hakikanin ayyuka."

Baya ga ingancin abinci da tarbiya, 'yan majalisar sun kuma ba da shawarwari dangane da kyautata tsarin samar da isassun gidajen kwana, sa kaimi kan tabbatar da yin amfani da albarkatun kiwon lafiya cikin adalci, tabbatar da kawo albarka cikin kwanciyar hankali, yin rigakafin kamuwa da cututtuka sakamakon wasu sana'o'i masu hadari, kiyaye halaltattun hakkokin 'yan ci rani, nakasassu, tsofaffin da suka yi ritaya, da 'yan kwadagon da suka bar masana'antun da ke mallakar gwamnati sakamakon gyare-gyaren da aka yi, da dai makamantansu. Hukumomin da abin ya shafa sun dora muhimmanci kan wadannan shawarwari, sun kuma karbe su gaba daya. An labarta cewa, tun daga shekarar bara, 'yan majalisar CPPCC sun gabatar da shawarwarin da suka shafi zaman rayuwar jama'a fiye da 1700, haka kuma, hukumomin da abin ya shafa sun karbi wasiku daga 'yan majalisar da fararen hula, da kuma ziyarar da suka yi har sau dubu 42 ko fiye. 'Yan majalisar CPPCC na taka rawar a-zo-a-gani wajen taimakawa gwamnati ta fuskar kara fahimtar ra'ayoyin jama'a, warware rikici, da kiyaye kwanciyar hankali da jituwa a kasar ta Sin.

A sakamakon bunkasuwar yanar gizo ta Internet, 'yan majalisar sun fara juya hankali kan yin mu'amala da jama'a ta hanyar Internet. Yanzu suna tattara ra'ayoyin jama'a tare da gabatar da shawarwarinsu ta yadda za a sauraron ra'ayoyin jama'a ta hanyar zamani. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China