in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Zhaoxing ya yi bayani kan tsarin shari'a da aikin sojoji na kasar Sin
2011-03-04 16:31:45 cri

Ranar Jumma'a 4 ga wata, kakakin taro na 4 na zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar na 11 Sin Li Zhaoxing ya shedawa manema labaru cewa, ya zuwa yanzu, an kafa cikakken tsarin shari'a a kasar Sin wanda ya dace da halin da kasar ke ciki na bunkasa tattalin arziki da al'umma.

Li Zhaoxing ya ce, bayan iyakacin kokarin da bangarori daban-daban suka yi, Sin ta cimma nasara sosai wajen tsai da dokoki. A shekarar 1982, Sin ta kyautata wasu abubuwan dake cikin kundin tsarin mulkin kasa har sau hudu bisa tsarin mulkin kasa na yanzu. Ya zuwa karshen watan Fabrairu na bana, Sin ta tanadi ayoyin tsarin mulkin kasa 239, ayoyin ka'idoji sama da 690, dokokin wuraren daban-daban kimanin 8600.

Ban da wannan kuma, Li Zhaoxing ya ce, yanzu Sin ta kafa wani tsarin shari'a na musamman da ya dace da tsarin gurguzu nakasar Sin dake bisa tushen tsarin mulkin kasa wanda ke dogara da shari'a, ka'idoji, dokokin wuraren daban-daban da dai sauran dokokin da suka shafi fannoni daban-daban.

Bayan da wannan kuma, game da aikin sojoji, Mr Li ya bayyana cewa, kafin karshen wannan shekara, yawan kasafin kudin da ake kebewa a fannin aiki sojoji ya kai kimanin kudin Sin RMB biliyan 601, wanda ya yi kasa da yawan kudin da sauran yawancin kasashen duniya suke kashewa. Aikin sojoji na kasar Sin burinsa shi ne kiyaye 'yancin kasar, da cikakken yanki, da ba zai kawo barzana ga ko wace kasa ba.(Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China