in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kafofin yada labaru na kasashen waje suna mai da hankali kan "Taruka biyu" na kasar Sin
2011-03-04 09:21:07 cri

A ran 3 ga wata, an kaddamar da taro a karo na hudu na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa na 11 a birnin Beijing. Kana za a kaddamar da taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a ran 5 ga wata. A cikin 'yan kwanankin da suka gabata, kafofin yada labaru na kasashen waje sun mai da hankali kan bude "Taruka biyu" na Sin, haka ma shirin shekaru 5 a karo na 12 da za a yi nazari a gun taruka biyu.

Jaridar The New York Times ta Amurka ta ba da labarin cewa, za a fitar da sabon shirin shekaru 5 na kasar Sin a wadannan taruka biyu, wanda zai canza hanyar bunkasa tattalin arziki daga fitar da kayayyaki masu dimbin yawa zuwa ketare da kuma zuba jari da dama ga manyan ayyukan amfanin jama'a zuwa kara bukatun jama'a cikin gida.

Kamfanin dillancin labaru na Reuter ya ba da labarin cewa, a cikin wannan shiri na shekaru biyar, za a dora muhimmanci kan rage fitar da gurbatacciyar iska da ruwa, da sa kaimi ga amfani da makamashi mai tsabta da makamashin da za a iya sake yin amfani da shi.

Bayan haka, kamfanin dillancin labaru na KyoTo na kasar Japan ya ba da labarin cewa, a cikin shirin shekaru 5 a karo na 12, shugabannin kasar Sin za su kokarta rage gibin dake tsakanin masu kudi da masu fama da talauci, tare da yin kwaskwarima ga tattalin arziki ta hanyar kara bukatun jama'a cikin gida.

Jaridar The Daily Telegraph ta Birtaniya ta ba da bayanin edita cewa, fitaministan kasar Sin Wen Jiabao ya bayyana cewa, kamata ya yi a kwatanta kwarewar jami'ai kan rike mulki bisa jin dadin zaman rayuwar jama'a, wannan ya yi nuni da cewa, za a kwatanta kwarewar jami'ai bisa rayuwar jama'a a maimakon karuwar tattalin arziki a nan gaba.

Dadin dadawa, kamfanin dillancin labaru na Yonhap ya ba da labarin cewa, a cikin tarukan biyu, za a fi dora muhimmanci kan kyautata rayuwar jama'a, tare da neman samun hanyar daidaita matsalolin hauhawar farashin kayayyaki da na gidaje da dai sauransu.

Bisa labarin da jaridar Chosun Daily ta kasar Koriya ta Kudu ta bayar, an ce, gwamnatin kasar Sin ta yi watsi da manufar da ta bi a da ta neman karuwar tattalin arziki cikin sauri. A maimakon haka, tana kokarin gudanar da ayyuka, ta yadda dukkan jama'ar kasar Sin za su iya more kyakkyawan sakamakon da aka samu ta hanyar bunkasa tattalin arziki cikin adalci.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China