in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar CPPCC za ta yi kokarin ba da shawara kan yadda za a aiwatar da shirin raya kasar Sin
2011-03-03 19:35:30 cri

A maraicen ranar 3 ga wata, an kaddamar da taro na 4 na babban kwamitin karo na 11 na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin (CPPCC), a babban dakin taro na jama'a da ke birnin Beijing, hedikwatar kasar Sin, inda wasu shugabannin kasar gami da 'yan majalisar 2182 suka halarci bikin bude taron.

Jia Qinglin, shugaban majalisar CPPCC, ya yi bayani kan aikin da aka yi a bara a madadin zaunanen kwamitin majalisar, haka kuma ya bayyana ayyukan da majalisar za ta yi a wannan shekara da cewa, majalisar za ta yi kokarin ba da shawara kan yadda za a aiwatar da wani shiri na shekaru biyar-biyar da aka tsara a karo 12 domin raya tattalin arziki tare da inganta rayuwar al'umma a kasar Sin.

A shekarar da ta gabata, 'yan majalisar CPPCC ta kasar Sin sun ba da shawarwari kan yadda za a tsara shirin raya kasar, tare da kiyaye saurin bunkasuwar tattalin arziki. Game da hakan, Mista Jia ya nuna wa majalisar babban yabo a jawabinsa.

'Yadda majalisar CPPCC ta ba da shawarwari kan aikin tsara shirin raya kasa ya zama wani misali na yin amfani da tsarin dimokuradiyya don tattara ra'ayoyin bangarorin daban daban, ta yadda za a iya aiwatar da manufofi masu inganci ga jama'a.'

1 2
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China