in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jihar Ningxia na kokarin yada tambarin abincin halal a duniya
2011-02-19 21:09:44 cri
Ibrahim: A nan kasar Sin, a duk lokacin da aka ambaci jihar Ningxia, abin da yake fitowa cikin zukatan mutane shi ne tsaunukan nan na Helan masu tsayi sosai da tumaki da shanu dake zama a filayen ciyayi da kuma kabarin sarkin daular Xia ta yamma da ake kiran shi Dala ta Gabas. Amma jama'a masu sauraro, ko kun san cewa, jihar Ningxia ta kuma shahara sosai ta fuskar samar da abincin halal, kuma jihar tana kokarin yada tambarin abincin halal don yada al'adun musulmai da suke zaune a kasar Sin ga kasashen duniya.

Sanusi: e, malam Ibrahim, ko ka san cewa, jihar Ningxia ba ta da girma, kuma yawan mutanen da suke zaune a jihar miliyan 6 ne kawai, amma yawan musulmai ya kai sulusi guda daga cikinsu. Wadannan musulmai suna mai da hankali sosai wajen samar da abincin halal. Game da wannan batu, madam Ma Fengxia wadda ke aiki a kwamitin kula da harkokin kabilu na birnin Yinchuan, wato babban birnin jihar Ningxia tana mai cewa, a ganin kabilar Hui wadda ke bin addinin Musulunci, abincin halal alama ce da ke bayyana yadda ake yada al'adun kabilar, inda ta bayyana cewa, "Abincin halal wani muhimmin abu ne ga musulmai. A cikin shekaru dubu 1 ko fiye da suka gabata, musulmai na kabilar Hui wadanda suke zaune a yankunan yammacin kasar Sin ba su canza ka'idarsu ta cin abincin halal ba ko kadan."

Ibrahim: Bugu da kari, sauran mutane wadanda ba su bin addinin Musulunci, amma suke zaune a jihar Ningxia suna girmama al'adar rayuwar musulmai da abinicinsu. Madam Hong Meixiang, shugabar majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta birnin Yinchuan ta gaya wa wakilanmu cewa, yawan dakunan samar da abincin halal da ake da su a jihar Ningxia ya kai fiye da kashi 90 cikin dari. Madam Hong tana mai cewa, "A nan jihar Ningxia, idan akwai wani musulmi a cikin mutanen da suke son cin abinci tare, to, tabbas ne dukkansu su shiga dakin samar da abincin halal gaba daya."

Sanusi: mun gane cewa, musulmai suna bin ka'ida kwarai lokacin da suke dafa abincin halal. Sabo da haka, gwamnatin kasar Sin ta fito da jerin manufofi masu gatanci a kokarin kare abincin halal da kuma bunkasa masana'antun samar da abincin halal. A ganin gwamnatin kasar Sin, irin wadannan manufofin da ta dauka wani muhimman matakai ne ga kokarin kiyaye ikon da kabilun da suke bin addinin Musulunci suka samu. Madam Ma Fengxia ta kara da cewa, "Lokacin da musulman kabilar Hui wadanda suke zaune a jihar Ningxia suke zabar kayayyakin yin abinci da adana da kuma sarrafa su, suna bin ka'idojin addinin musulunci kamar yadda aka tsara, ba a karya doka ko kadan ba."

Ibrahim: Jama'ar kabilar Hui dake zaune a jihar Ningxia sun gaji fasahohin sarrafa abinci bisa ka'idojin addinin Musulunci daga kakani da kakani. Ya zuwa yanzu, sun riga sun nakalci fasahohin sarrafa abincin da musulmai wadanda suke zaune a jihar Xingxia suke bukata. Irin wadannan abincin halal sun zama alamun dake alamta wannan jihar wadda ke arewa maso yammacin kasar Sin.

Sanusi: Birnin Wuzhong da ake kiran shi "garin abincin halal na kasar Sin", wuri ne da yawan musulami ya kai fiye da kashi 50 cikin kashi dari na yawan jimillar mutanen jihar. Sabo da haka, ana kokarin bunkasa sana'ar samar da abincin halal a birnin don raya tattalin arzikin wannan birni.

Ibrahim: Kamfanin samar da naman halal na Laoheqiao dake birnin Wuzhong wani muhimmin kamfani ne na kasar Sin ta fuskar samar da naman shanu da na tumaki. Yawan naman da yake samarwa a kowace shekara ya kai kusan ton dubu 4. Wani direktan wannan kamfani ya gaya wa wakilinmu cewa, "Limaminmu suna yanka shanu da tumaki bisa ka'idojin da musulmai suke bi kamar yadda ya kamata, wato kawunan shannu da na tumaki su kan kalli yamma, wato wurin da Makka ko alkibla take."

Sanusi: Lokacin da aka yi gasar wasannin motsa jiki ta kasashen Asiya a birnin Guangzhou a watan Nuwamba na bara, wannan kamfani ya samu kwangilar samar da naman shanu da na tumaki ga 'yan wasannin motsa jiki da jami'ai da 'yan jaridu wadanda suke bin addinin Musulunci. Yawan naman da wannan kamfani ya samar a lokacin gasar ya kai ton 300.

Ibrahim: Jama'a masu sauraro, a birnin Wuzhong, ba ma kawai kamfanin Laoheqiao ya yi suna sosai ba, har ma kamfanin "Desert Prince", wato wani kamfani na daban dake samar da naman shanu da na tumaki ya shahara kwarai a dimbin kasashe masu bin addinin Musulunci. A bara, ya samu wata kwangilar samar da nama daga hannun hukumar kula da harkokin aikin haji. Bisa wannan kwangila, a cikin shekaru 5 masu zuwa, wannan kamfani zai samar wa wasu mahajjata kayan lambu da naman shanu da na kaji a kowace shekara. Yawan kudin da wannan kamfani zai samu a kowace shekara bisa wannan kwangila zai kai kudin Sin yuan miliyan 265.

Sanusi: malam Ibrahim, ba ma kawai wadannan kamfanoni sun shahara sosai ta fuskar samar da naman shanu da tumaki da musulmai suke bukata ba, har da wani abincin da aka yi da naman tumaki da ya yi suna sosai a jihar. Lokacin da ake dafa irin wannan abinci, da farko dai, ana jefa wasu naman tumaki da aka wanke shi sosai a cikin ruwan zafi, sannan sai a sa wasu kayayyakin ka-fi-zabo a ciki. Musulmai na kasar Sin, har ma da masu yawon bude ido wadanda ba su bin addinin Musulunci suna jin dadin cin irin wannan nama. Madam Hong Meixiang, shugabar majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta birnin Yinchuan, ta gaya wa wakilinmu cewa, musulmai na kabilar Hui dake zaune a jihar Ningxia suna maraba da abokai masu yawon bude ido su zo jihar don su ci irin wannan naman tumaki, inda madam Hong Meixiang ta ce, "Zan raka abokai masu yawon bude ido zuwa dakunan cin abinci na halal domin su dandana abincinmu. A cikin irin wadannan dakunnan cin abinci, adon da aka yi, da kalaman maraba da zuwan baki da tufafin da ma'aikata suke sanye da shi da kuma abinci iri iri dukkansu suna bayyana al'adun kabilar Hui gaba daya."

Ibrahim: madam Ma Fengxia wata jami'ar ofishin kula da harkokin kananan kabilu na jihar Ningxia ta bayyana cewa, yawan musulmai wadanda suke zaune a duk fadin kasashen duniya ya kai kusan biliyan 1.3. Sabo da haka, yawan kayayyakin abincin da sauran kayayyakin da suke biyan bukatun musulmai, kuma ake bukata a kasuwa yana ta karuwa a kowace shekara. Hakan ya sa gwamnatin jihar Ningxia ta fito da "ka'idojin tabbatar da ingancin abincin halal" a shekarar 2009. Ya zuwa yanzu, wasu kasashe masu bin addinin Musulunci sun riga sun amince da wadannan ka'idodin da jihar Ningxia ta kasar Sin ta tsara. Madam Ma Fengxia ta bayyana cewa, "Wasu kasashen Larabawa da kasashe masu bin addinin Musulunci sun aika da wakilansu zuwa jiharmu a kokarin fahimtar ka'idojin da muka tsara, kuma muke aiwatawar lokacin da muke sarrafa abincin halal. Suna ganin cewa, ka'idojin sarrafa abincin halal da muke aiwatarwa suna dacewa da ka'idojin addinin Musulunci. Sakamakon haka,kamfanoninmu suka samu kwangiloli da yawa daga wadannan kasashe masu bin addinin Musulunci."

Sanusi: jama'a masu sauraro, yanzu abincin halal da jihar Ningxia take fitarwa zuwa ketare ya riga ya zama wata alamar dake wakiltar al'adun musulmai na kasar Sin. Sauran kasashe masu bin addinin Musulunci sun soma fahimtar kabilar Hui da al'adun musulmai da al'adun addinai na kasar Sin, har ma da manufofin kabilu da kasar Sin take aiwatarwa. Sannan tattalin arzikin jihar Ningxia ya samu ci gaba ta hanyar bunkasa kamfanonin sarrafa abincin halal. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China