Sanusi: Amma, me ya sa babban bankin kasar Sin ya dauki wannan matakin kara kudin ruwa a lokacin da ake murnar Ranar Kirismati a kasashen yammacin duniya? Game da wannan tambaya, Mr. Ba Shusong ya kara da cewa, "Babban bankin kasar Sin ya dauki wannan mataki ne a lokacin da jama'ar kasashe masu arziki suke hutu, wannan zai ba su damar samun isashen lokacin nazarin manufarmu a kokarin magance illar da za a kawo wa kasuwannin kasa da kasa sakamakon wannan manufa."
Ibrahim: A jajibirin ranar da aka sanar da kara kudin ruwa, babban bankin kasar Sin ya bayyana dalilin da ya sa na sake aiwatar da manufar kudi da za ta zauna bisa gindinta. Babban bankin kasar Sin ya bayyana cewa, shekarar 2011 shekara ce da za a soma aiwatar da sabon shirin shekaru biyar-biyar na bunkasa tattalin arziki da zaman al'ummar kasar. Wurare daban daban na kasar suna da kwadayin samun rancen kudi a kokarin neman bunkasuwa cikin sauri. Sakamakon haka, za a fuskanci matsin lambar karin yawan rancen kudin da ake bukata. Sabo da haka, babban bankin kasar Sin ya dauki matakin karin yawan kudin ruwa a kokarin tabbatar da niyyarsa ta kayyade saurin raguwar darajar kudin. Game da tasirin da wannan mataki zai yi a bangaren batun darajar kudi, madam Zuo Xiaolei wadda ke nazarin harkokin tattalin arziki a kamfanin hada-hadar kudi na Yinhe tana mai cewa, "Buri mafi muhimmanci da ake son cimmawa ta hanyar aiwatar da manufar kudi shi ne kayyade saurin raguwar darajar kudi. Sabo da haka, tabbas ne a dauki wannan matakin kara yawan kudin ruwa don kayyade saurin raguwar kudin Sin. Yanzu haka ana fuskantar matsin lambar raguwar darajar kudin Sin sosai."
Sanusi: Bugu da kari, a kwanan baya, madam Hu Xiaolian, mataimakiyar gwamnan babban bankin kasar Sin ta bayyana cewa, babban bankin zai ci gaba da daukar matakai iri daban daban a nan gaba a kokarin taka muhimmiyar rawa a fannin manufofin kudi a kasuwa. Mr. Li Daokui, mamban kwamitin tattauna manufofin kudi na babban bankin kasar Sin ya kuma yi hasashen cewa, mai yiyuwa ne babban bankin kasar Sin zai ci gaba da kara yawan kudin ruwa a shekarar 2011, inda Mr. Li ya bayyana cewa, "Har yanzu yawan kudin ruwan da muke karba kashi 3 ne cikin kashi dari kawai. Amma a kan gano cewa, idan saurin hauhawar farashin kayayyaki ya kai fiye da kashi 3 cikin kashi dari, wannan ya alamta cewa, an soma shiga lokacin raguwar darajar kudi ke nan. Sabo da haka, muna da damar kara yawan kudin ruwa a shekarar 2011."
Ibrahim: malam Sanusi, sabo da yanzu ana fuskantar matsalar raguwar darajar kudi. Wannan mataki ya bayyana niyyar saukar da farashin kayayyaki ta gefen babban bankin kasar Sin. Malam Sanusi, kana jin wannan mataki zai yi tasiri ga kasuwar cinikin gidajen kwana?
Sanusi: mai yiyuwa ne, amma ba ni da irin wannan ilmin tattalin arziki. Yanzu bari mu gayyaci Mr. Li Wenjie, babban direktan sashen kula da kasuwannin yankunan arewacin kasar Sin na kamfanin cinikin gidaje na Zhongyuan da ya bayyana mana tasirin da wannan mataki zai yi wa kasuwar cinikin gidajen kwana.
"Wannan mataki ba zai yi tasiri ga kasuwar cinikin gidajen kwana nan da nan ba, amma bayan da aka kara yawan kudin ruwa a wannan karo, za a canza ra'ayoyin jama'a ta fuskar zuba kudinsu a nan gaba." (Sanusi Chen)