"Arim! Bismillah ka ba ni tsire in ci!"
"To!"
Masu sauraro, muryar da kuka saurara dazu, murya ce ta wani dan kabilar Uyghur mai suna Arim, wanda ke sayar da tsire a kan titi dake garin Bijie na lardin Guizhou dake kudu maso yammacin kasar Sin. Kwanan baya, a wata gasar fidda nagartattun mutane da aka yi ta yanar gizo wato Intanet a nan kasar Sin, Mista Arim ya samu kuri'u mafi yawa har ya zama nagartaccen mutumin da ya burge al'ummar kasar Sin a shekara ta 2010, lamarin da ya sa ya zama jarumi a cikin zukatan jama'ar kasar Sin. A cikin shirinmu na wannan mako, za mu gabatar muku da wani bayani dangane da wannan mutum dan kabilar Uyghur mai suna Arim.
Mista Arim, mai shekaru 39 da haihuwa, dan asalin gundumar Hejing ta jihar Xinjiang ne, wanda ya bar gida lokacin yana da shekaru 20 da haihuwa. Ya je birane da dama, ciki har da Urumqi, Beijing, Chongqing, Kunming, gami da wasu biranen dake lardin Guizhou, a karshe ya yanke shawarar neman aiki a garin Bijie na lardin Guizhou.
A lokacin zafi na shekara ta 2001, Arim ya isa garin Bijie, inda ya ari kudin Sin Yuan dari 1 daga shugaban wani gidan shan giya dake wurin, don kafa wani shagon sayar da tsire. A wancan lokaci, Arim ya kan samu Yuan 20 ko 30 a kowace rana ta sayar da tsire. Bayan mako guda, ya mayar da Yuan darin da ya ara a wajen wannan mai gidan shan giya. A nasa bangaren, mai gidan shan giyar Mista Liu Jiong ya gayawa wakilinmu cewa:
"A karshen shekara ta 2001 ne, Arim ya zo garin Bijie, kuma babbar matsalar da ya fuskanta ita ce zaman rayuwa. A wancan lokaci, ba shi da kudi ko kadan, don haka na ba shi aron Yuan dari daya. Sa'an nan yayi amfani da wannan kudi don raya sana'arsa, kuma nan yake cin abinci yake kuma zama."
Daga baya, Arim ya fara sana'arsa ta gasa tsire. Yayin da yake yin mu'amala tare da mazauna garin Bijie, Arim ya ji dadin zumuncin da suka nuna masa, inda ya ce:
"Daga baya na gamu da mutane da dama a garin Bijie, wadanda suka nuna himma da kwazo wajen taimaka mini."
Zumunta gami da kulawar da mazauna garin Bijie suka nuna masa, sun sa Arim ya bullo da wani ra'ayi na taimakawa sauran mutane, da bayar da gudummawa gwargwadon karfinsa ga zamantakewar al'umma. Don haka, Arim ya yanke shawarar yin amfani da kudin da ya samu daga sana'arsa ta sayar da tsire a kokarin tallafawa daliban da suke fama da matsalar karancin kudin karatu, kuma daliban kwalejin Bijie sun kasance dalibai da Arim ya dade yana ba su tallafi. Daga cikin daliban, wani mai suna Zhou Yong ya bayyana cewa:
"Ina daya daga cikin daliban dake fama da matsalar karancin kudin karatu da Mista Arim ke tallafawa. Watakila ban san wasu manyan ayyukan da Mista Arim ke tafiyarwa ba, amma na san halayyarsa, gami da yadda zaman rayuwarsa yake. Ya taba gaya mini cewa, ya kamata mu himmatu wajen taimakawa sauran mutane."
A shekara ta 2006, Arim ya kai kudin Sin Yuan dubu 5 wanda ya samu daga sana'ar gasa tsire ga sashin tallafawa dalibai na kwalejin Bijie, inda ya bukaci da a bada tallafi ga daliban dake fama da kangin talauci, lamarin da ya burge malaman kwalejin kwarai da gaske. A karshe, kwalejin Bijie ya baiwa wannan kason kudi sunan "kyautar kudin karatu na Arim".
A nasa bangaren, mataimakin sakataren reshen jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin dake kwalejin Bijie Mista Tang Yuhua ya gayawa wakilinmu cewa:
"Mun ji kamshin tsire a takardun kudin da Mista Arim ya bayar. A wancan lokaci, mun kidaya yawan kudin da ya bayar. Tsire nawa ne Arim ya sayar ya samu Yuan dubu 5? Daga baya, na yi shawarwari tare da shugaban kwalejinmu Mista Zhang, inda muka yanke shawarar kara bayar da tallafin Yuan dubu 5, don kafa wani asusun tallafawa dalibai da aka lakaba masa sunan 'Arim'."
A cikin 'yan shekarun nan, mazauna garin Bijie suna nuna cikakken goyon-baya ga sana'ar Mista Arim, inda su kan je cin tsire a shagonsa. Tun daga shekara ta 2006, an fara amfani da "kyautar kudin karatu na Arim" don tallafawa dalibai 20 a kowace shekara. A halin yanzu, yawan tallafin kudin da bangarori daban-daban suke bayarwa a kwalejin Bijie ya ninka sau 10, kuma akwai mutane da dama wadanda suka yi koyi daga Arim don bayar da tallafin kudi ga dalibai masu fama da talauci.
A cikin shekaru 10 da yake zaune a garin Bijie, Arim ya sayar da gasasshen tsire da yawa, kuma yayi amfani da kashi 80 bisa dari na kudin da ya samu don tallafawa dalibai masu fama da kangin talauci. An ce, jimillar kudin tallafin da ya bayar ta zarce Yuan dubu 100, har ma yawan daliban da suka samu tallafi daga wajensa ya wuce dari. Bugu da kari kuma, Mista Arim ya nuna hazaka sosai wajen tallafawa mutanen da bala'u daga Indallahi suka shafa a sassa daban-daban na kasar Sin. Bayan abkuwar bala'in girgizar kasa a gundumar Yushu ta lardin Qinghai na kasar Sin a shekara ta 2010, Mista Arim ya sayi abubuwa da kayayyakin da darajarsu ta kai Yuan dubu 8, sa'an nan ya tafi da su zuwa gundumar Yushu, a kokarin kafa tantuna, da tura kayayyakin yaki da bala'in girgizar kasa tare da sojoji.
Amma har zuwa yanzu, Arim yana zaune ne a cikin wani tsohon daki mai murabba'in mita 40 kawai. Irin wannan abun da Mista Arim yayi ba ma kawai ya burge jama'ar garin Bijie ba, haka kuma ya burge dukkan al'ummar kasar Sin.
A shekara ta 2007, Arim ya zama daya daga cikin muhimman mutane 10 dake lardin Guizhou, sa'an nan a shekarar da ta gabata wato shekara ta 2010, an zabe shi don ya zama abun koyi na kyakkyawar halayya a lardinsa. Har wa yau kuma, kwanan baya, a wata gasar fidda nagartattun mutane wadanda suka burge al'ummar kasar Sin a shekara ta 2010 da aka yi ta yanar gizo wato Intanet, Arim ya samu mafi yawan kuri'un da aka jefa har ya zama na farko a gasar.
A waje daya kuma, labarin Mista Arim yana yaduwa cikin sauri ta hanyar Intanet, wanda ke jawo hankalin masu amfani da Intanet sosai, haka kuma sun nuna babban yabo gare shi. Daya daga cikinsu ya bayyana cewa:
"A matsayinsa na dan asalin jihar Xinjiang, kana wani dan kasuwa dake gudanar da harkoki a waje, kamata yayi mu yi koyi daga Arim, da yin kokarin tallafawa mutanen da suke bukatar taimako."
A halin da ake ciki yanzu, Mista Arim yayi suna sosai a yankin Bijie, har ma sana'arsa ta gasa tsire na samun ci gaba sosai. Amma duk da haka, yana nan yana ci gaba da tallafawa daliban dake fama da kangin talauci.(Murtala)