in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hu Jintao ya yi kira da a kulla huldar kawance tsakanin Sin da Amurka
2011-01-21 16:08:23 cri

A ranar 20 ga wata, yayin da yake halartar liyafar da kungiyoyin aminan kasar Sin da ke Washington D.C. na kasar Amurka suka shirya masa, Hu Jintao, shugaban kasar Sin, wanda ke ziyara a kasar, ya yi jawabin cewa, kamata ya yi, Sin da Amurka su yi kokari tare don kulla wata huldar kawance tsakaninsu, tare da bin manufar girmama juna, da samun moriya tare.

Hu Jintao ya ce, kokarin kyautata huldar da ke tsakanin kasashen 2 ya dace da babbar moriyar jama'arsu, haka kuma ya kasance wani sharadin da ake bukatar cikawa kafin a wanzar da zaman lumana da ci gaba a duniya. A nata bangare, kasar Sin za ta tsaya kan manufar bude kofa ga kasashen waje, da nacewa ga hanyar raya kasa tare da tabbatar da zaman lumana. Kasar za ta ci gaba da kokarin kiyaye wani yanayi na zaman lafiya a duniya, don ta raya kanta, haka zalika, a kokarin da take na samun ci gaba, kasar na da gudunmawar da za ta bayar ta fuskar kiyaye zaman lafiya a duniya.

Ban da haka kuma, don neman kara kyautata huldar da ke tsakanin Sin da Amurka, Hu Jintao ya shawarci bangarorin 2 da su nuna hangen nesa da sanin ya kamata a fannin karfafa hadin kan kasashen 2, da kokarin samar da wani sabon yanayi na amfanawa juna da cin moriya tare game da hadin gwiwa a fannin tattalin arziki, da kara tuntubar juna da mu'amala kan yadda za a tinkari wasu manyan kalubale da suka shafi duniya, gami da girmama juna da zaman daidaiwa daida, da yin hattara wajen kulawa da wasu batutuwan da ka iya ta da fitina a tsakaninsu. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China