in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masu sauraronmu daga Afrika da yammacin Asiya suna dora muhimmanci kan ziyarar Hu Jintao
2011-01-21 15:16:22 cri

Shugaban kasar Sin Hu Jintao ya kai ziyarar aiki daga ran 18 zuwa ran 21 ga wata a kasar Amurka. Gidan rediyon kasar Sin wato CRI ya bayar da labaru game da wannan ziyara a dukkan fannoni. A kwanan baya, masu sauraron CRI sun aiko da wasiku ko ta hanyar Email domin nuna fatan alheri ga ziyarar Hu Jintao.

Wani mai sauraro daga kasar Nijeriya Nuraddeen Ibrahim Adamu ya aiko da wasika cewa, a cikin shekaru 10 masu zuwa, kasar Sin za ta zama kasuwa mafi girma a duniya. Yana fatan shugaban kasar Sin Hu Jintao zai cimma nasarar wannan ziyara.

Ban da haka kuma, masu sauraro daga kasashen Algeria da Turkiyya sun bayyana cewa, kasashen Sin da Amurka kasashe ne mafi muhimmanci a duniya, hadin gwiwar kasashen biyu zai taka rawa mai yakini kan tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya. Bayan rikicin hada-hadar kudi, kudin Sin RMB zai kara taka muhimmiyar rawa kan cinikin kasa da kasa kamar dalar Amurka.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China