in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hu Jintao ya gana da magajin gari na birnin Chicago Richard Daley
2011-01-21 14:48:39 cri

A ran 20 ga wata, a birnin Chicago, shugaban kasar Sin Hu Jintao da ke yin ziyara a kasar Amurka ya gana da magajin garin birnin Chicago Richard Daley.

Hu Jintao ya bayyana cewa, aikin bunkasa dangantakar da ke tsakanin kasashen Sin da Amurka ya dangana ne da goyon baya da jama'a da bangarori daban daban na kasashen biyu suka bayar. Yanzu, da akwai larduna da jihohi 36 wadanda suka kulla dangantakar abokantaka a tsakanin kasashen biyu, kuma akwai birane 161 daga kowa ne bangare wadanda suka kulla dangantakar abokantaka, larduna daban daban na kasashen biyu sun yi hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki da ba da ilmi da sauransu. Kuma yana fatan birnin Chicago zai yi amfani da kwarewarsa don ci gaba da yin hadin gwiwa tare da bangaren Sin a fannonin makamashi da aikin kiyaye muhalli da sa kaimi ga yin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.

Richard Daley ya bayyana cewa, yana fatan birnin Chicago zai zama birni da zai hada kai sosai tare da kasar Sin. Kuma ya kara da cewa, yana fatan birnin Chicago zai kara samu jarin da kamfanonin kasar Sin za su zuba, da kara samun masu 'yawon shakatawa daga kasar Sin.(Abubakar)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China