in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kafofin watsa labaru na kasashen waje sun nuna babban yabo ga ziyarar da Hu Jintao ya yi a kasar Amurka
2011-01-21 10:07:01 cri

Tun daga ran 18 ga wata da shugaban kasar Sin Hu Jintao ya kai ziyara a kasar Amurka zuwa yanzu, kafofin watsa labaru na kasashen waje suna mai da hankali sosai kan ziyararsa, kuma suna nuna babban yabo ga ziyarar.

Bisa labarin da jaridar The Wall Street Journal ta bayar, an ce, ziyarar da Hu Jintao ya kai a kasar Amurka za ta kafa sabuwar dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu. Kuma bisa yarjejeniyoyi a jerin da bangarorin biyu suka kulla, za a sa kaimi ga bunkasa dangantakar da ke tsakaninsu.

Jaridar Los Angeles Times ta bayyana cewa, shugabannin biyu sun amince da cewa akwai bambancin ra'ayoyi a fannonin tattalin arziki da hakkin bil Adam a tsakanin kasashen biyu, amma sun yi alkawarin cewar za su kara yin hadin gwiwa, ta haka, dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu za ta kara samun bunkasa.
Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na AFP ya bayar, an ce, a gun ziyarar da Hu Jintao ya yi, kasashen biyu sun kulla yarjejeniyoyi a jeri wadanda suka shafi kudin Amurka dala biliyan 45.

Bisa labarin da jaridar Der Spiegel na kasar Jamus ta bayar, an ce, shawarwarin da shugabannin kasashen Sin da Amurka suka yi ya shaida cewa, kasashen biyu sun mai da hankali sosai kan dangantakar da ke tsakaninsu, kuma suna son kara yin kokari wajen warware rikicin da ke tsakaninsu.

Bisa labarin da jaridar The India Times ta bayar, an ce, ziyarar da Hu Jintao ya yi a kasar Amurka tana da muhimmiyar ma'ana ga kasa da kasa. Wannan ya shaida cewa, karfin kasar Sin ya karu, kuma kasar Amurka ta kara fahimtar muhimmiyar ma'ana ta yin hadin gwiwa tare da kasar Sin.Bisa labarin da jaridar Estadao De Sao Paulo ta bayar, an ce, dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka ita dangantaka ce mafi muhimmanci a karni na 21. Kasashen Sin da Amurka suna son yin amfani da wannan ziyara wajen sake kara fahimtar juna.(Abubakar)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China