in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hu Jintao ya gana da John Boehner da Harry Reid
2011-01-21 09:54:28 cri

A ran 20 ga wata a birnin Washington, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya gana da shugaban majalisar wakilan kasar Amurka John Boehner da shugaban jam'iyyar dake samun rinjaye a majalisar dattijai ta kasar Amurka Harry Reid.

Inda Hu Jintao ya furta cewa, ba ma kawai kyakkyawar huldar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka ta dace da moriyar jama'ar kasashen biyu ba, hatta ma ta ingiza tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da wadata a yankin Asiya da Pacific. Moriyar kasashen Sin da Amurka tana kan matsayi mafi muhimmanci. Kasar Sin tana son kara yin musayar ra'ayi da zurfafa hadin gwiwa a tsakaninta da kasar Amurka bisa hangen nesa domin girmamawa juna da kawo moriyar juna.

Bugu da kari, shugaba Hu Jintao ya jaddada cewa, idan kasashen Sin da Amurka suka bude kofa ga juna da kara yin hadin gwiwa, huldarsu a fannin tattalin arziki da ciniki za ta kara samun ci gaba, ta yadda za a kawo moriyar jama'ar kasashen biyu.

A madadin 'yan jam'iyyu biyu na majalisar wakilai ta kasar Amurka, John Boehner ya nuna matukar maraba da zuwan shugaban kasar Sin Hu Jintao, kuma ya jaddada cewa, bunkasuwar huldar kasashen biyu ta kawo moriya ga bangarorin biyu. Kana Harry Reid ya ce, ya nuna maraba da zuwan Mr. Hu Jintao a majalisar dattijai ta kasar Amurka. 'Yan majalisar dattijai ta kasar Amurka sun dora muhimmanci sosai kan huldar dake tsakanin kasashen biyu. Majalisar dattijai ta kasar Amurka tana son taka rawa mai yakini kan aikin zuba jari da kasar Sin ta yi a kasar Amurka.

A ran 20 ga wata da yamma, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya isa birnin Chicago, wanda girmansa ya dauki matsayi na 3 daga cikin biranen kasar Amurka, domin ci gaba da yin ziyarar aiki.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China