in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta ci gaba da maraba da kamfannonin kasashen waje da su zuba jari a kasar Sin in ji Hu Jintao
2011-01-20 21:12:26 cri

Ran 19 ga wata, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya nuna cewa, kasar Sin tana maraba da kamfannonin kasashen waje da su zuba jari a kasar Sin. Kasar Sin za ta ci gaba da yin gyare-gyare a cikin gida da kuma bude kofa ga kasashen waje, tare da ci gaba da inganta matakan zuba jari da za su kasance masu adalci ga kamfannonin kasashen waje ciki har da kamfannonin kasar Amurka.

Shugaba Obama na kasar Amurka ya nuna cewa, kasar Amurka na fitar da kayayyaki da gudanar da aikin hidima zuwa kasar Sin, Amurka ta sami moriya sosai daga kyakkyawar dangantaka tsakanin kasashen biyu. Kuma kamfannonin kasar Sin sun kafa rassansu a kasar Amurka, wannan ya sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin kasar Amurka. Ya jaddada cewa, kamfannonin kasar Sin suna da kyakkyawar makoma a kasar Amurka, yana fatan masana'antu da 'yan kasuwa na kasashen biyu za su ci gaba da yin hadin gwiwa. [Musa Guo]

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China