Ran 18 ga wata ne, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya sauka Washington, babban birnin kasar Amurka, inda ya fara ziyara aiki a kasar. Kafofin watsa labaru na kasa da kasa sun mai da hankali sosai kan ziyarar Hu Jintao a kasar Amurka, kuma sun yaba ga ziyara tasa.
A wannan rana, yawancin manyan kafofin watsa labaru na kasar Amurka sun bayar da cikkaken rahotanni kan ziyarar Hu Jintao. Gidan telibijin na CNN na kasar Amurka ya ruwaito bayanan babbar sakatariyar harkokin waje ta kasar Amurka Hillary Clinton cewa, tattalin arzikin kasashen Amurka da Sin suna cudar juna, haka ma kuma makomar kasashen biyu.
Kamfanin dillancin labaru na AFP na kasar Faransa ya bayar da rahoto cewa, ziyarar shugaba Hu Jintao ta alamta cewa dangantaka tsakanin kasashen biyu ta kai wani sabon mizani.
Kamfanin dillancin labaru na Reuter ya ce, matsayin tattalin arzikin kasar Sin ya zama na biyu a duniya, ziyarar shugaba Hu Jintao a kasar Amurka a wannan karo ta kasance ziyara mafi muhimmanci a cikin shekaru 30 da suka wuce. [Musa Guo]