in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin kasashen Sin da Amurka sun cimma daidaito kan raya dangantakar abuta tsakaninsu
2011-01-20 17:33:48 cri
Ranar 19 ga wata, a fadar White House, shugaban kasar Sin Mista Hu Jintao da takwaransa na kasar Amurka Barack Obama sun yi shawarwari, inda suka bayar da wata hadaddiyar sanarwar dake cewa, sun cimma matsaya kan kokarin raya dangantakar abokantaka ta hadin-gwiwa dake girmamawa juna da kawo moriya a tsakaninsu.

Ranar 19 ga wata da safe, a fadar White House dake birnin Washington na kasar Amurka, shugaban kasar Amurka Barack Obama ya shirya wani gagarumin biki don maraba da Mista Hu Jintao, wanda ke ziyara a kasar, inda aka rera taken Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin, tare da harba bindiga har sau 21 don nuna girmamawa. Wannan shi ne karo na farko da shugaban kasar Sin ya kai ziyarar aiki a kasar Amurka, tun bayan da Barack Obama ya hau karagar mulkin kasar.

A cikin 'yan shekarun nan, huldar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka na samun ci gaba cikin sauri. A watan Nuwamban shekara ta 2009, Barack Obama ya kawo ziyara kasar Sin, lamarin da ya nuna cewa shi ne shugaban kasar Amurka na farko wanda ya kawowa kasar Sin ziyara a cikin shekarar da ya hau ragamar mulkin kasar. A yayin da yake nan kasar Sin, shugabannin kasashen biyu sun bayar da wata hadaddiyar sanarwa, inda suka jaddada cewa, za su dukufa ka'in da na'in kan raya dangantakar hadin-gwiwa ta dukkan fannoni a tsakaninsu cikin karni na 21. Amma a shekarar da ta gabata, wato shekara ta 2010, an gamu da matsaloli da dama wajen raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Amma, a halin da ake ciki yanzu, wadanne matakai za'a dauka domin kara samun fahimtar juna tsakanin kasashen Sin da Amurka, kuma yadda za'a yi domin a karfafa hadin-gwiwa tsakaninsu batutuwa ne dake da muhimmanci kwarai gare su.

A ranar 19 ga wata, Mista Hu Jintao da Mista Barack Obama sun jagoranci manyan jami'an kasashen biyu a fannonin tattalin arziki, cinikayya, da diflomasiyya da sauransu don gudanar da shawarwari kusan na tsawon sa'o'i uku. A yayin shawarwarin, Mista Hu Jintao ya jaddada cewa, yayin da ake kara fuskantar kalubale a duniya, kamata yayi kasashen Sin da Amurka su kara daukar nauyin dake kansu, kuma hadin-gwiwar dake tsakaninsu na da babbar ma'ana gare su har ma ga duniya baki daya. Mista Hu ya ce:

"Kamata yayi kasashen Sin da Amurka su girmama mulkin kansu, cikakken yankinsu, gami da babbar moriyarsu, a kokarin bunkasa dangantakar kasashen biyu yadda ya kamata, da kara bayar da babbar gudummawa ga shimfida zaman lafiya a duniya baki daya. Mun cimma daidaito kan nuna hazaka wajen kara raya dangantakar kasashen biyu, ta yadda za'a samar da alheri ga jama'ar kasashen biyu har ma ga jama'ar sauran kasashen duniya."

A nasa bangaren kuma, a wurare da dama, ba sau daya ba kuma ba sau biyu ba shugaban kasar Amurka Barack Obama ya jaddada cewa, kasarsa na fatan ci gaba da inganta hadin-gwiwa tare da kasar Sin, inda ya ce:

"Kasar Amurka tana maraba da ci gaban da kasar Sin ke samu, wadda ta zama wata kasa mai karfi kuma mai wadata a duniya. Nasarorin da kasar Sin ta samu suna samar da alheri ga jama'ar kasashen biyu a fannin tattalin arziki, haka kuma hadin-gwiwa dake tsakaninsu na taimaka wa sosai wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Asiya da tekun Pasifik har ma a duniya baki daya."(Murtala)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China