Sanusi: a cikin shekaru 5 da suka gabata, aikin gona ya samu ci gaba sosai a kasar Sin. Kuma yankunan karkara sun samu sauye-sauye kwarai, manoma ma sun samu moriya yadda ya kamata. A shekarar 2010, jimillar amfanin gona da kasar Sin ta samu ta wuce ton miliyan dari 5, kuma kasar Sin ta yi girbin amfanin gona cikin shekaru 7 a jere. A nan kasar Sin a kan bayyana cewa, wadatuwar abinci kan kwantar da hankalin jama'a. Sabo da haka, tabbatar da samar da isashen abinci ga jama'a ya zama nauyi mafi muhimmanci da aka dora wa bangaren aikin gona a nan kasar Sin. Mr. Han Changfu, ministan aikin gona na kasar Sin yana mai cewa, "Batun gonaki tamkar wani layi ne da ba za a iya tsallake shi ba, wato dole ne yawan gonakin da ake samarwa a kasarmu ya wuce hektoci miliyan 120, ba za a iya rage yawansu ba. Sannan dole ne a kebe gonakin da yawansu ya kai hektoci miliyan dari 1 daga cikinsu domin noman hatsi, shi ma ba za a iya rage shi ba."
Ibrahim: bugu da kari, a yayin wannan taro, an nuna cewa, har yanzu ba a iya yin ban ruwa kamar yadda ya kamata ga rabin gonaki a nan kasar Sin ba. Sabo da haka, an sanya aikin inganta ayyukan ban ruwa a matsayin wani muhimmin aikin da za a aiwatar shi a nan gaba. Mr. Chen Lei, ministan albarkatun ruwa na kasar Sin ya ce, a cikin shekaru 5 masu zuwa, gwamnatin kasar Sin za ta mai da hankali kan muhimman batutuwa hudu game da ayyukan ban ruwa, wato za ta inganta ayyukan ban ruwa wadanda aka dade ana amfani da su, kuma suka lalace, sannan za ta hanzarta warware irin wadannan ayyukan da suke da nasaba da rayuwar jama'a. Haka kuma za ta kara sa ido kan yadda ake amfani da ruwa. Bugu da kari, za ta hanzarta yin gyare-gyare kan manufofin samar da kuma yin amfani da ayyukan ban ruwa.
Sanusi: amma yanzu kasar Sin na fuskantar hali mai sarkakiya ta fuskar bunkasa tattalin arziki. Dalilai iri iri da suke kawo cikas ga kokarin bunkasa aikin gona suna ta karuwa. Mr. Li Guoxiang wanda ke nazarin ci gaban yankunan karkara a nan kasar Sin ya ce, "Yanzu muna kokarin tabbatar da yawan gonakin da muke bukata dan kiyaye masu sana'ar aikin gona. A cikin 'yan shekarun nan, manoma sun mai da hankali sosai kan aikin gona sabo da gwamnatin kasar Sin ta samar musu tallafin kudin, kuma ta kan sayi hatsi daga hannun manoma bisa farashin da suka tsara cikin kwangila."
Ibrahim: A gaban halin da ake ciki ta fuskar aikin gona a yankunan karkara, a yayin wannan taron da gwamnatin kasar Sin ta shirya ta fuskar yankunan karkara da aikin gona, an nuna cewa, ya kamata a tabbatar da ganin manoma sun samu moriya da karin guraban aikin yi da yawan kudin shiga da za su samu ya karu. Madam Tang Min, mataimakiyar shugaban asusun Youcheng (友成) tana mai cewa, "A ganina, magana mafi muhimmanci a gabanmu ita ce maganar kara yawan kudin shiga da masu sana'ar aikin gona suke samu. Bayan yawan kudin shiga da manoma suke samu ya karu, za a iya inganta rayuwar jama'a a fannoni daban daban. Yanzu hanyar warware wannan matsala da ta fi dacewa ita ce rage yawan manonan da suke aiki a yankunan karkara, wato ya kamata a shigar da wasu manoma cikin garuruwa da birane. Sakamakon haka, yawan gonakin da manoma wadanda za su ci gaba da zama a yankunan karkara za su samu zai iya karuwa, sannan dole ne a yi kokarin sanya manoma wadanda suke zaune a garuruwa da birane su samu aikin yi, kuma daga karshe su zama mazauna garuruwa da birane. Bugu da kari, dole ne a tabbatar da ganin sun samu inshorar kiwon lafiya, kuma yaransu sun shiga makaranta kamar yadda ya kamata." (Sanusi Chen)