Hu Jintao ya nuna babban yabo ga gudummawa da Bill Clinton ya bayar wajen bunkasa dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, kuma ya bayyana cewa, a halin da ake ciki, kasashen Sin da Amurka suna da moriyar da za su samu a fannoni da yawa. Ya kamata a kara fahimtar juna a fannin siyasa da kara yin hadin gwiwar tattalin arziki da kara yin mu'amala a tsakanin jama'ar kasashen biyu, da kara nuna adalci a manyan batutuwan duniya.
Bill Clinton ya bayyana farin cikinsa sosai na ganin shugaban kasar Sin Hu Jintao ya ziyarci kasar Amurka. Kuma ya bayyana cewa, ya yi kokari sosai wajen kara samar da yanayin fahimtar juna a tsakanin kasashen biyu, da kara yin hadin gwiwa da warware bambancin ra'ayoyi a tsakaninsu.(Abubakar)