in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin kasashen Sin da Amurka sun cimma daidaito a tsakaninsu
2011-01-20 10:31:14 cri

A ranar 19 ga wata, a fadar White House ta kasar Amurka, shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao da takwaransa na kasar Amurka Barack Obama sun yi shawarwari a tsakaninsu, inda suka cimma daidaito da cewa, kasashen biyu za su yi kokarin dukufa ka'in da na'in wajen raya dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa da girmama juna da samun moriyar juna tsakaninsu, haka kuma shugabannin kasashen biyu sun tsara makomar raya dangantakar kasashen biyu a zuwa gaba da zurfafa hadin gwiwa ta bangarorin biyu, sun samu ra'ayi daya tsakaninsu.

Hu Jintao ya yaba da hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen Sin da Amurka kan manyan batutuwan duniya da na shiyya shiyya tare da batutuwan dangatakar kasashen biyu, musamman ma bayan da shugaban kasar Amurka Barack Obama ya hau karagar mulki, kuma ya bayyana cewa, kamata ya yi a raya dangantakar kasashen biyu bisa sabon tunani da daukar sabbin matakai.

Haka kuma Mr. Hu ya jaddada cewa, kamata ya yi a inganta fahimtar da amincewar juna ta hanyar yin shawarwari tsakaninsu, don rage rashin fahimtar juna da damuwa tsakaninsu da yin hadin gwiwa don sa kaimi ga samun bunkasuwa da wadata da inganta moriyar juna a tsakaninsu. Haka kuma dole ne bangarorin biyu su girmama hanyar samun bunkasuwa da tsarin zamantakewar al'umma da aka zaba, da girmama mulkin kai na kowanensu da kiyaye cikkakken yankin kasashen biyu da raya moriyarsu. Haka kuma ta fuskar tattalin arziki da cinikayya, kamata ya yi kasashen Sin da Amurka su ci gaba da daidaita manufofin tattalin arziki daga manyan fannoni, don samu da yalwata hadin gwiwa ta moriyar juna.

Hu Jintao ya ce, kamata ya yi kasashen Sin da Amurka su inganta hadin gwiwa a tsakaninsu kan batun zirin Koriya da na nukiliyar kasar Iran, da batun sauyin yanayi da sauran batutuwa da dama da ke kawo kalubale a duniya.

Obama ya bayyana cewa, kasar Amurka tana fatan yin kokari tare da kasar Sin, don inganta tuntubar manyan jami'ai tsakaninsu, da sa kaimi ga amincewar juna bisa manyan tsare-tsare tsakaninsu don warware matsalar bunkasa tattalin arziki ta dogon lokaci da sa kaimi ga inganta hadin gwiwa don samun wadatar yankunan Asiya da Fasific da dukkan duniya baki daya. Ya ce, kasar Amurka tana fatan daidaita batutuwan tattalin arziki da cinikayya da kasar Sin ta dora muhimmanci sosai a kai da yin kokari don samun ci gaba a wannan fanni.

Haka kuma Obama ya sake jaddada cewa, Amurka tana kula da manufar kasar Sin daya tak a duniya, kuma za ta tsaya tsayin daka kan hadaddun sanarwoyi 3 da aka daddale tsakaninsu, kuma Amurka tana farin cikin da ganin kyautatuwar dangantakar gababi biyu a tsakanin mashigin tekun Taiwan, kuma tana fatan dagantakar da ke tsakaninsu za ta ci gaba da samun bunkasuwa.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China