in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Sin da Amurka sun ba da hadaddiyar sanarwa a tsakaninsu
2011-01-20 09:45:17 cri

A ranar 19 ga wata, a birnin Washington na kasar Amurka, kasashen Sin da Amurka sun ba da hadaddiyar sanarwa a tsakaninsu, inda suka jaddada cewa za a dukufa ka'in da na'in don yin hobbasa wajen raya dangantakar kasashen biyu a cikin karni na 21 daga dukkan fannoni, haka kuma sun nuna cewa, za su yi kokari tare don bunkasa dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa da girmama juna da samun moriyar juna tare, ta hakan za a raya moriyar kasashen biyu, don fuskantar dama da kalubalen da ke kasancewa a cikin karni na 21.

Haka kuma sanarwar ta ce, bangarorin biyu za su inganta dangantakar kasashen biyu, da daidaita batutuwan da bangarorin biyu suka dora muhimmanci sosai a kai, kuma za su tabbatar da alhakin da ke kansu a kasashen duniya, da bayyana matsayin da suke tsayawa a kai game da batun yankin Taiwan da na hakkin dan Adam da huldar sojojin kasashen biyu, kana, bangarorin biyu za su sa kaimi ga mu'amalar manyan jami'ai a tsakaninsu, da jaddada muhimmancin mu'amalar majalisu biyu a tsakaninsu, haka kuma kasashen biyu za su inganta shawarwari da tattaunawa tsakaninsu don tinkarar kalubalen duniya da na shiyya-shiyya, don gina dangantakar abokantakar tattalin arziki ta samun moriyar juna da inganta shawarwari da hadin gwiwa wajen tsara manufofin tattalin arziki daga manyan fannoni, da ingiza yin ciniki da saka jari ba tare da shingaye ba, da yaki da ra'ayin ba da kariya ga ciniki, don sa kaimi ga samun dangantakar cinikayya cikin daidaito, tare da yin hadin gwiwa wajen kiyaye ikon mallakar fasaha da tsarin hada-hadar kudi na duniya, haka kuma bangarorin biyu sun amince da inganta hadin gwiwa tsakaninsu wajen warware batun sauyin yanayi, makamashi, kiyaye muhalli, da yalwata mu'amalar jama'a a tsakaninsu.

Haka kuma shugabannin kasashen Sin da Amurka sun bayyana cewa, ziyarar shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao a kasar Amurka za ta kara ingiza dangatakar kasashen biyu, kuma kyakkyawar dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka za ta dace da moriyar jama'ar kasashen biyu, kuma za ta amfanawa yankunan Asiya da Fasific da dukkan duniya baki daya.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China