in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Sin da Amurka sun yi kokarin samun damar yin hadin gwiwa a yayin zaman taron dandalin makamashi maras gurbata muhalli
2011-01-19 16:38:24 cri

A ran 18 ga wata a Washington, babban birnin kasar Amurka, an bude taron dandalin tattaunawa kan makamashi maras gurbata muhalli a karo na biyu a tsakanin kasashen Sin da Amurka. Kwamitin nazarin tsarin kirkiro sabbin kayayyaki da samun bunkasuwa na kasar Sin da kwalejin Brookings ta kasar Amurka su ne suka jagoranci zaman wannan dandali, mataimakin shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin Dong Jianhua da ministan kimiyya da fasaha na kasar Sin Wan Gang da jakadan kasar Amurka dake kasar Sin Jon Huntsman da ministan makamashi na kasar Amurka Steven Chu da sauran manyan jami'ai fiye da dari daya na gwamnatocin kasashen biyu da na kamfannonin kasashen ne suka halarci zaman taron wannan dandali na tattaunawa. A cikin kwanaki masu zuwa, mahalartar taron za su tattauna kan hadin gwiwar a tsakanin kasashen Sin da Amurka a fannin samar da makamashi maras gurbata muhalli da huldar dake tsakanin kasashen biyu na shekaru 10 masu zuwa.

Bayan da aka cimma nasarar yin dandalin tattaunawa makamashi maras gurbata muhalli a tsakanin kasashen Sin da Amurka a karo na farko a watan 10 na shekarar 2009 a birnin Beijing na kasar Sin, yanzu, ana yin zaman taron wannan dandalin tattaunawa ne a karo na biyu a albarkacin ziyara da shugaban kasar Sin Hu Jintao ke yi a kasar Amurka. Shugaban kasar Sin Hu Jintao da takwaransa na kasar Amurka Barack Obama sun aika da wasikun taya murna, inda suka jaddada muhimmin matsayin hadin gwiwarsu a fannin samar da makamashi maras gurbata muhalli.

Ministan kimiyya da fasaha na kasar Sin Wan Gang ya jaddada a gun taron cewa, samar da makamashi maras gurbata muhalli ya zama aiki mafi kyau a game da kasashen Sin da Amurka wajen yin hadin gwiwa, ya ce,

"Kasashen biyu kasashe ne dake bukatar samun makamashi mai dimbin yawa, kuma suna kan gaba wajen fitar da iska mai dumama yanayi, sabo da haka, ya kamata kasashen biyu su yi hadin gwiwa domin yin nazari a fannin kimiyya da fasahar wajen amfani da makamashi maras gurbata muhalli."

A wannan rana kuma, an yi bikin kafuwar cibiyar nazarin makamashi maras gurbata muhalli ta kasashen Sin da Amurka, wadda shugabannin kasashen Sin da Amurka suka yanke shawarwar kafa ta a shekarar 2009 a yayin da Mr. Barack Obama ya ziyarci kasar Sin. Ministan makamashi na kasar Amurka Steven Chu ya bayyana a wajen bikin cewa, kasashen Sin da Amurka suna bukatar yin kokari tare domin ciyar da wannan cibiya gaba. Ya kara da cewa,

"A cibiyar nazarin makamashi maras gurbata muhalli ta kasashen Sin da Amurka, kwararru daga kasashen biyu za su iya haduwa domin tattauna batutuwan daidaita hanyar sarrafa makamashi maras gurbata muhalli."

Yanzu, hukumomin da abin da ya shafa na kasashen biyu sun zabi ayyukan nazari kan ma'adanin kwal maras gurbata muhalli da motoci maras gurbata muhalli da kuma gine-ginen dake iya yin tsimin makamashi. Jami'ar kimiyya da fasaha ta tsakiyar kasar Sin ta nuna kwarewa sosai a fannin nazari kan ma'adanin kwal maras gurbata muhalli, ta kulla wata yarjejeniyar hadin gwiwa a gun bikin. Shugaban wannan jami'a Li Peigen ya bayyana cewa,

"Gwamnatin kasar Sin ta kara ware kudi don wannan aiki, kana manyan kamfannoni su ma sun kara ware kudi, jami'armu za ta yi kokari kan nazari domin biyan bukatun gwamnatin kasar."(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China