in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
(Sabunta)Shugaban kasar Sin ya isa birnin Washington na kasar Amurka
2011-01-19 15:36:17 cri

A ran 18 ga wata, bisa gayyatar shugaban kasar Amurka Barack Obama, takwaran aikinsa na kasar Sin Hu Jintao ya isa birnin Washington, hedkwatar Amurka domin yin ziyara a wannan kasa.

A cikin jawabin da ya yi a filin saukar jiragen sama, shugaba Hu ya yi fatan alheri ga jama'ar kasar Amurka, tare da isar da gaisuwa da jama'ar Sin suke yi musu. Ya ce, babban makasudinsa na kai ziyara a Amurka a wannan karo shi ne nuna kara amincewa da juna da sada zumunci, da karfafa hadin gwiwa tsakaninsu, a kokarin sa kaimi ga bunkasa dangantakar hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Amurka a karni na 21 a duk fannoni. Sin tana fatan bunkasa dangantaka tsakaninsu cikin yakini ta hanyar girmama juna da samun moriyar juna, a kokarin sa kaimi ga shimfida zaman lafiya da kwanciyar hankali cikin dogon lokaci da samun wadata tare da sauran sassan kasa da kasa baki daya.

A wannan rana da dare, Shugaba Hu ya halarci liyafar da Barack Obama ya shirya masa a fadarsa ta White House. Bangarorin biyu sun nuna babban yabo ga sakamakon da aka samu a fannin dangantaka tsakanin Sin da Amurka, tare da nuna fatansu na kara sa kaimi ga bunkasa dangantakar hadin gwiwa tsakaninsu a duk fannoni bisa wannan ziyara.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China