in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya isa birnin Washington na kasar Amurka
2011-01-19 09:14:26 cri

A ran 18 ga wata, bisa gayyatar shugaban kasar Amurka Barack Obama, takwaran aikinsa na kasar Sin Hu Jintao ya isa birnin Washington, hedkwatar Amurka domin yin ziyara a wannan kasa.

Mataimakin shugaban kasar Amurka Joe Biden, jakadan Amurka a Sin Jon Huntsman da uwargidansa, wasu manyan jami'an Amurka da suka hada da babban darektan kula da harkokin Asiya na kwamitin tsaron kasa na fadar shugaban kasar Amurka Jeff Bader da sauransu, jakadan Sin a Amurka Zhang Yesui da dai makamantansu su ne suka marabci shugaba Hu da 'yan rakiyarsa a filin saukar jiragen sama.

A wajen shugaba Hu ya yi jawabin cewa, yanzu ana samun babban sauyi a kasa da kasa. Matakan samun moriyar juna a tsakanin Sin da Amurka na karuwa a yau da kullum, haka ma alhakin da su kan dauka tare. A sabili da haka kasashen biyu za su samu makoma mai kyau a nan gaba wajen hada gwiwa a tsakaninsu. Babban makasudinsa na kai ziyara a Amurka a wannan karo shi ne nuna kara amincewa da juna da sada zumunci, da karfafa hadin gwiwa tsakaninsu, a kokarin sa kaimi ga bunkasa dangantakar hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Amurka a karni na 21 a duk fannoni. Sin tana fatan bunkasa dangantaka tsakaninsu cikin yakini ta hanyar girmama juna da samun moriyar juna, a kokarin sa kaimi ga shimfida zaman lafiya da kwanciyar hankali cikin dogon lokaci da samun wadata tare da sauran sassan kasa da kasa baki daya.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China