in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabunta: An kafa tsarin kafofin watsa labaru na kasa da kasa na kasar Sin wato CIBN
2011-01-18 22:33:40 cri

Jama'a masu sauraro. Yanzu lokaci ya yi da za mu gabatar muku da shirinmu na A ganin CRI. A cikin shirinmu na yau za mu gabatar muku da bayani dangane da kaddamar da tsarin kafofin watsa labaru na kasa da kasa na kasar Sin wato CIBN.

Ran 18 ga wata a nan birnin Beijing, an yi bikin kaddamar da kafar watsa labaru na kasa da kasa ta kasar Sin (CIBN) da kamfanin kula da kafofin watsa labaru na kasa da kasa, Wannan ya alamta cewa, gidan rediyon CRI wanda ke da tarihi na shekaru 70 ya shiga wani sabon mataki na gudanar da aikinsa na watsa labarai da shirye-shirye ta sabbin hanyoyin sadarwa daga dukkan fannoni.

A ran 18 ga wata ne aka yi bikin kafa tsarin kafofin watsa labaru na kasa da kasa na kasar Sin CIBN a birnin Beijing, inda aka yi kide-kide da raye-raye. wannan ya alamta cewa, an kaddamar da wani dandalin watsa labaru ta harsuna 61, ta hanyoyin sadarwa iri iri, da salon bude kofa. Mr. Wang Guoqing mataimakin direktan ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin, da Mr. Tian Jin mataimakin direktan hukumar kula da harkokin telebiji, da rediyo da fina-finai ta kasar Sin, da wasu daruruwan manyan baki sun halarci bikin kafa tsarin na CIBN.

Shugaba Wang Gengnian na CRI ya yi jawabi a bikin, inda ya nuna cewa, tsarin CIBN wani tsari ne na tafiyar da kafofin watsa labarai na kasar Sin ta hanyar yanar gizo, wayar tafi da gidanka da sauran sabbin hanyoyin sadarwa na zamani, kuma zai watsa labarai cikin harsuna da dama zuwa fadin duniya. Mr. Wang Gengnian ya ce,

"A matsayinsa na wani dandalin watsa labarai ta sabbin hanyoyin sadarwa da ke hada kasar Sin da sauran kasashen duniya, tsarin na CIBN zai gudanar da ayyukansa bisa ka'idojin "nuna matsayin kasar Sin, mai hangen nesa a duniya, da kula da abubuwan da ake ji a rai", ma'aikata daga sassan harsuna 61 za su yi kokarin inganta shirye-shiryen telebiji ta yanar gizo, da telebiji da rediyo na wayar tafi da gidanka, da rediyon tafi da gidanka ta sabbin hanyoyin sadarwa da sauran ayyuka ta hanyoyi iri iri."

Tsarin kafofin watsa labarun kasa da kasa na kasar Sin mai suna CIBN ya kasance kafar watsa labarai ta farko a kasar Sin, wadda ke kunshe da hanyoyin sadarwa iri-iri, kuma ke watsa labarai cikin harsuna da dama.

Mataimakin babban edita na gidan rediyon kasar Sin CRI, Ma Weigong ya bayyana cewa, kaddamar da tsarin CIBN na taimakawa wajen biyan bukatun bunkasuwar hukumomin watsa labarai.

'Ci gaban kafofin watsa labarai, da na sana'ar watsa labarai, sun kasance babban kalubale ga kafofin watsa labarai na zamani a duniya, abun da ya sa kafofin watsa labarai da dama ke nuna hazaka wajen neman yin gyare-gyare, da lalubo sabuwar hanyar da za su bi wajen tafiyar da ayyukansu, ta yadda za ta dace da zamani.'

Domin kyautata tsarin gudanar da tsarin na CIBN, ya sa an kafa kamfanin kula da kafofin watsa labaru na kasa da kasa a wannan rana, da nufin samar da wani muhimmin dandamalin da zai nuna goyon baya ga ayyukan gudanar da tsarin CIBN, da kuma gabatar da kudin da yake bukata. Shugaban rediyon CRI, Wang Gengnian ya bayyana cewa,

'Kafa kamfanin kula da kafofin watsa labaru na kasa da kasa zai taka rawa kan karfafa hadin gwiwa tsakanin bunkasuwar kafofin watsa labaru da gudanar da harkokin masana'antu, kuma kamfanin zai bude wani sabon shafi wajen bunkasuwar CRI a tsawon tarihinsa.'

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China