in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kafa tsarin kafofin watsa labaru na kasa da kasa na kasar Sin wato CIBN
2011-01-18 20:03:19 cri

Ran 18 ga wata a nan birnin Beijing, an yi bikin kaddamar da kafar watsa labaru na kasa da kasa na kasar Sin (CIBN) da kamfanin kula da kafofin watsa labaru na kasa da kasa, Wannan ya alamta cewa, gidan rediyon CRI wanda ke da tarihi na shekaru 70 ya shiga wani sabon mataki na gudanar da aikinsa na watsa labarai da shirye-shirye ta sabbin hanyoyin sadarwa daga dukkan fannoni.

Mr. Wang Guoqing mataimakin direkatan ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin, da Mr. Tian Jin mataimakin direktan hukumar kula da harkokin telebiji, da rediyo da fina-finai ta kasar Sin, da wasu daruruwan manyan baki sun halarci bikin kafa tsarin na CIBN.

Shugaba Wang Gengnian na CRI ya yi jawabi a bikin, inda ya nuna cewa, tsarin CIBN wani tsari ne na tafiyar da kafofin watsa labarai na kasar Sin ta hanyar yanar gizo, wayar tafi da gidanka da sauran sabbin hanyoyin sadarwa na zamani, kuma zai watsa labarai cikin harsuna da dama zuwa fadin duniya. Ya yi nuni da cewa, kafa tsarin CIBN wata muhimmiyar nasara ce da CRI ya samu. A cikin shekaru 5 masu zuwa, tsarin CIBN zai taka muhimmiyar rawa a fannin kafofin watsa labaru na duniya.

Bisa labarin da muka samu, an ce, za a gudanar da ayyukan tsarin CIBN bisa ka'idojin "nuna matsayin kasar Sin, mai hangen nesa duniya, da kula da abubuwan da ake ji a rai", ma'aikatan daga sassan harsuna 61 za su yi kokarin inganta shirye-shiryen telebiji ta yanar gizo, da telebiji da rediyo na wayar tafi da gidanka, da rediyon tafi da gidanka ta sabbin hanyoyin sadarwa da sauran ayyuka ta hanyoyi iri iri. (Musa Guo)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China