in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana begen ziyarar da shugaban kasar Sin Hu Jintao zai yi a kasar Amurka
2011-01-18 16:52:42 cri
A ran 18 ga wata da yamma, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya tashi daga birnin Beijing na kasar Sin zuwa kasar Amurka don yin ziyarar aiki bisa gayyatar da shugaban kasar Amurka Barack Obama ya yi masa. Ba kamar yadda a kan yi ba a lokutan baya, a farkon sabuwar shekara, shugaban kasar Sin ya kai ziyararsa ta farko a kasar Amurka wadda ta fi karfin tattalin arziki a duniya, sabo da haka, al'ummu a sassan duniya sun dora muhimmanci sosai kan wannan ziyara, kuma ana begen sakamakon da za a samu a yayin ziyarar.

Bisa jadawalin da ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ta fitar a kwanan baya, an ce, shugaban kasar Sin Hu Jintao zai fara ziyara a kasar Amurka daga ran 18 zuwa ran 21 ga wata, kuma zai ziyarci biranen Washington da Chicago. Kuma ziyarar da Mr. Hu zai kai a birnin Washington ta fi han hankalin al'ummu a sassan duniya.

A cikin shekaru biyu da Barack Obama yake rike da ragamar mulkin kasar Amurka, ko da yake ya gana da shugabannin kasashe da yawa, amma firaministan kasar India Manmohan Singh da shugaban kasar Mexico Felipe Calderon su kadai ne suka kai ziyarar aiki a kasar Amurka. Kasar Amurka ta bayyana muradin yin matukar maraba da zuwan Mr. Hu Jintao, kuma za ta shirya bikin yin maraba da liyafar kasa.

Ganawar da za a yi tsakanin Mr. Hu Jintao da Mr. Barack Obama tana jawo hankalin al'ummun sassan duniya sosai. Wani birnin na daban da Mr. Hu Jintao zai kai ziyara shi ne birnin Chicago, wanda yake a matsayi na 3 daga cikin manyan biranen kasar Amurka, kana ya zama cibiyar zirga-zirgar jiragen ruwa, na kasa da na sama wacce ta hada da gabashin kasar da kuma yammacinta. Ban da haka kuma, birnin Chicago shi ne tushen masana'antun kasar Amurka, a nan ne aka kafa kamfanin Motorola ne a shekarar 1928. Ba kamar yadda Mr. Hu Jintao zai ziyarci birnin Washinton D.C ba, zai ziyarci birnin Chicago ne domin musayar ra'ayi kan zaman rayuwar jama'a.

Tun daga lokacin da Mr. Obama ya gayyaci Mr. Hu Jintao zuwa kasar Amurka a yayin taron koli da aka yi a shekarar da ta gabata a birnin Toronto, al'uumun sassan duniya suka dora muhimmanci sosai a kan wannan ziyara. A yanayin duniyar dake bunkasuwa cikin sauri, ta yaya kasashen Sin da Amurka za su samu karin bunkasa? Kuma ta yaya za su kara yin hadin gwiwa domin tinkarar kalubaloli daban daban? Musayar ra'ayi da kasashen biyu za su yi a kan manufofinsu ya fi muhimmanci. Bayan da rikicin hada-hadar kudi ya barke a karshen shekarar 2008, shugabannin kasashen Sin da Amurka sun kara azama wajen tuntubar juna ta hanyoyin ganawa da aika wasiku da buga waya da sauransu. Huldar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka ta zama huldar diplomasiyya mafi muhimmanci a duniya, tana haifar da babban tasiri ga duk kasashen duniya.

A hakika dai, ana begen ganin irin yarjejeniyoyin da bangarorin biyu za su kulla. A yayin da ministan harkokin waje na kasar Sin Yang Jiechi ya kai ziyara a watan Janairu na bana a kasar Amurka, ya bayyana cewa, a yayin wannan ziyara, bangarorin biyu za su kulla jerin yarjejeniyoyi a fannonin tattalin arziki, ciniki, makamashi, muhalli, al'adu, kimiyya da sauransu.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China