Bisa labarin da ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ta bayar, an ce, a yayin ziyarar ta kwanaki 4, Hu Jintao zai isa birnin Washington, kuma shugabannin kasashen biyu za su yi shawarwari kan batutuwan da suke fi daukar hankalinsu. Kuma Hu Jintao zai gana da manyan jami'an majalisar dokokin kasar Amurka, da yin mu'amala tare da bangarori daban daban. Daga baya, Hu Jintao zai kai ziyara birnin Chicago.
Bana shekara ce ta cika shekaru 40 da samun farfadowar dangantakar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu, bangarorin biyu sun mai da hankali sosai kan wannan ziyara. Bangaren Amurka ya bayyana cewa, zai yi matukar maraba da zuwan Mr. Hu Jintao, kuma za a shirya bikin maraba da liyafar karramawa ta kasa.(Abubakar)