"Ina fatan matsakaicin yawan GDP na kasar Sin ya kai matsayi na biyu a duniya, kana ya kai matsayi na biyu ta fuskar ba da tabbacin zaman rayuwar jama'a."
"Ingancin rayuwar jama'ar kasar Sin yana bayan na jama'ar Japan sosai. A hakika dai, za mu fuskanci kalubale iri iri muddin muna son kasancewa a matsayi na biyu."
Sanusi: Matsakacin saurin karuwar GDP na kasar Sin ya kai kashi 9 cikin kashi dari ko fiye a kowace shekara a tsakanin shekarar 1978 da ta 2009 sakamakon aiwatar da manufofin bude kofa da yin gyare-gyare kan tattalin arziki. Kuma yawan GDP ya kai dalar Amurka fiye da biliyan 4900 a shekarar 2009, amma har yanzu matsakaicin yawan GDP na kasar Sin yana kimanin matsayi na 100 ne a duniya, ingancin rayuwar Sinawa ma ya samu koma baya sosai idan an kwatanta shi da na kasashe masu arziki. Sabo da haka, Mr. Wen Jiabao, firaministan kasar Sin ya bayyana cewa, "An shafe dimbin shekaru ana tsara yadda za a zamanintar da kasar Sin, amma abubuwan zamani da hada da wasu matsaloli suna kasancewa tare, kuma tsofaffi da sabbin kalubale suna kuma kasancewa tare. Sakamakon haka, yanzu kasar Sin na fuskantar kalubalen da ba aka safai ake ga irinsu ba a da. A hakika dai, har yanzu Sin kasa ce mai tasowa."
Ibrahim: Wannan kalami haka yake, malam Sanusi. Jama'a ko gwamnatin kasar Sin, dukkansu sun gane cewa, Sin kasa ce mai dimbin mutane kuma maras neman ci gaba cikin daidaito wadda ke kokarin canja tsarin tattalin arzikinta, ta yadda za ta fuskanci kalubale sosai a nan gaba lokacin da take kokarin samun ci gaba.
Sanusi: malam Ibrahim ya kamata a fahimci cewa, a cikin dogon lokacin da ya gabata, kasar Sin ta kan yi kokarin neman ci gaba ne ta hanyoyin fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje da zuba jari a fannoni daban daban. Sakamakon haka, ba ta da karfi wajen kirkiro sabbin fasahohin zamani da sarrafa kasuwa. Wani abin misali mafi shahara shi ne kasar Sin ta iya sayen wani jirgin sama kirar Boeing bayan da ta fitar da riguna miliyan dari 5 zuwa ketare. Mr. Yao Shujie, shehun malami wanda ke koyar da ilmin tattalin arziki a jami'ar Nottingham ta kasar Birtaniya yana mai cewa, "Yanzu Sin tana dogara da makamashin halittu da danyun kayayyaki kawai a kokarin samun karuwar yawan GDP. Idan ana son yawan GDP ya sake ninka sau daya a nan gaba, tilas a canja wata sabuwar hanya. Dole ne kasar Sin ta canja hanyar bunkasa tattalin arzikinta maimakon na baya."
Ibrahim: A ganin shehu malami Yao, abin da ya wajaba shi ne kasar Sin ta kyautata ingancin tattalin arzikinta. Mr. Yao ya kara da cewa, "Da farko dai, ya kamata kasar Sin ta inganta fasahohin zamani domin inganta masana'antun kere-kere. Sannan dole ne a hanzarta raya sana'ar hidima a kokarin inganta rayuwar jama'a. Bugu da kari, dole ne a inganta aikin gona sabo da kasar Sin kasa ce mai dimbin mutane."
Sanusi: Yanzu kasar Sin tana tsara wani sabon shiri na shekaru biyar-biyar na raya tattalin arziki da zaman al'ummar kasar. Bisa wannan shiri, saurin karuwar GDP zai kai kashi 7 ko kashi 7.5 cikin kashi dari. Manazarta sun nuna cewa, matsayin da kasar Sin ke dauka yanzu ya yi kusan daidai da matsayin da kasar Japan ta dauka a tsakanin shekarar 1960 da ta 1969 na karnin da ya gabata. Amma a wancan lokaci, kasar Japan ta samu ci gaba sosai wajen samun daidaiton sake raba arzikin kasa ga jama'a, har ma ta kafa wani kyakkyawan tsarin ba da tabbaci ga jama'a. Amma har yanzu kasar Sin ba ta samu nasarar kawar da gibin dake kasancewa tsakanin masu arziki da marasa arziki ba, kuma aikin kafa tsarin ba da tabbaci ga jama'a yana kan matakin farko ne. Game da wannan batu, madam Zhang Ben'nan wadda ke aiki a cibiyar nazarin bayanan tattalin arziki ta kasar Sin ta bayyana cewa, "wannan halin da muke ciki ya sanya mu yi kokarin daidaita arziki a tsakanin jama'a a cikin shekaru 5 masu zuwa. Yanzu kasar Sin ta zama yanki mafi girma na biyu ta fuskar tattalin arziki a duniya, ba ma kawai kasarmu ta zama kasa mai karfi ba, hatta ma ya kamata jama'arta su zama jama'a masu arziki." (Sanusi Chen)