in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Amurka suna da kyakkyawar makoma kan tattalin arziki da ciniki
2011-01-17 20:24:48 cri

Ran 17 ga wata, jaridar "People's daily" ta gwamnatin kasar Sin ta bayar da labari cewa, ya zama wajibi a yi kokarin bunkasa huldar tattalin arziki da ciniki da ke tsakanin kasashen Sin da Amurka bisa manyan tsare-tsare da hangen nesa, wannan zai taimaka wajen kara moriyar jama'ar kasashen biyu har ma ya ba da gudummawa ga moriyar jama'ar duniya.

A cikin wannan labari na jaridar, an ce, ya zuwa shekarar 2020, mai yiyuwa ne kasuwar kasar Sin za ta zama kasuwa mafi girma a duniya, don haka za ta zama wata muhimmiyar dama ga masana'antu da 'yan kasuwa na kasar Amurka.

Labarin jarida ya jaddada cewa, yanzu ana cikin lokaci mai muhimmanci sosai ga bunkasuwar huldar tattalin arziki da ciniki na kasashen Sin da Amurka. Kyakkyawar huldar tattalin arziki da ciniki da ke tsakaninsu za ta sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikinsu da yunkurin farfadowar tattalin arzikin kasashen duniya. (Musa Guo)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China