in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Amurka ta samu alheri sosai a fannin yin ciniki tsakaninta da kasar Sin
2011-01-17 16:51:22 cri

Bisa sabbin alkaluman da ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin ta bayar a kwanan baya, an ce, a cikin 'yan shekaru da suka wuce, kasar Amurka ta samu alheri sosai a fannin yin ciniki tsakaninta da kasar Sin.

A cikin alkaluman da aka bayar, an ce, ya zuwa karshen shekarar 2010, yawan jarin da kasar Amurka ta zuba wa kasar Sin ya kai fiye da kudin Amurka dala biliyan 65, sannan akwai wasu kumafanoni bayar da hidima fiye da 100 na kasar Sin da ke samun jari daga kamfanonin kasar Amurka. Kuma bisa rahoton da kungiyar kasuwanin kula da ciniki da ke tsakanin Sin da Amurka ta bayar, an ce, yawan kamfanonin Amurka da ke kasar Sin da suka samu riba a shekarar 2009 ya kai kashi 71 cikin dari, daga cikinsu, yawan kamfanonin da suka samu riba daga kasar Sin ya fi wanda suka samu a kasashen waje kuma ya kai kashi 46 cikin dari.

A sa'i daya kuma, a matsayinta ta abokiyar cinikayya ta biyu ta kasar Amurka, kasar Sin ta kasance kasar ta Amurka ta fitar da kayayyaki cikin sauri. A cikin 'yan shekaru 10 da suka wuce, yawan ayyukan da kasar Amurka ta fita zuwa kasar Sin a sana'ar kera kayayyaki da amfanin gona ya karu da kashi 330 cikin kashi dari.(Abubakar)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China